DANGANTAKA TSAKANIN KATSINA DA SOKOTO.
- Katsina City News
- 22 Nov, 2024
- 161
Dangantaka tsakanin Katsina da Sokoto ta samo asaline a lokacin Jihadin Shehu Usman Danfodio na karni na (19). Tun kamin Jihadi akwai wasu daga cikin Malaman Katsina da sukayi Karatu a Gobir wajen Shehu Usman Danfodio da kuma dansa Muhammadu Bello, misali Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje yayi karatu a Gobir wajen Sarkin Musulmi Muhammad Bello da sauransu. Acikin shekarar 1804 ne aka gudanar Yakin Tafkin Kwato, tsakanin Rundunar Jihadi data Sarkin Gobir, Wanda su masu Jihadin a karkashin Jagorancin Mujaddadi Shehu Usman Danfodio sukayi nasara akan Sarkin Gobir, Tarihi ya nuna Malam Ummarun Dallaje ya halarci Yakin Tafkin Kwato daga Katsina. A sabili da wannan nasararre Shehu yayi Kira ga almajiranshi cewa su kaddamar da Jihadi a Garuruwan su.
A Katsina, Shugabanni ukku ne sukayi takakkiya wajen Shehu a Gobir domin a basu Tuta su kaddamar da Jihadi,wannan yana daya daga dangantakar Kasar Katsina da Sokoto.
Garin Sokoto an kafashine bayan an Kare Jihadi a wajen shekarar 1809, kamin wannan lokacin Shehu Yana zaune ne a Garin Sifawa. Garin Sokoto ya kafu sosai ne a cikin shekarar 1809, a lokacin da wurin ya Zama Mazaunin Muhamnad Bello, watau Dan Sarkin Mujaddadi Shehu Usman Danfodio, bayan da aka Kasa ita Daular gida biyu. Sashen Gabas karkashin kulawar Muhammad Bello, yayin da sashen Yamma yake karkashin kulawar Malam Abdullahi Gwandu, kanen Shehu Usman Danfodio, Wanda ya kafa babban birnin sa a Gwandu.
Bayan da Shehu ya kafa Daular Sokoto( Sokoto Chaliohate) sai sauran Garuruwan Daular da suka hada da Katsina, Kano, da Daura, Zaria, Adamawa, Ilorin da sauransu, suka koma karkashin ikon Sokoto, anan suke ansar Umarnin su, kuma suna Kai haraji duk shekara. Katsina kamar sauran Garuruwa, ta samu dangantaka Mai kyau da Sokoto, domin kuwa akwai girmama juna tsakanin su.
Bayan da aka Kare Jihadi a Katsina acikin shekarar 1807, sai aka raba Kasashe ga Shuwagabanin Jihadi, misali shi 1. Ummarun Dallaje shi ya Zama Sarkin Katsina. 2. Ummarun Dunyawa ya Zama Sarkin Sullubawa inda ya kafa babban birnin shi a Zandam 3. Sai Muhammad Dikko Dan Malam na Alhaji shi aka ba Sarautar Magajin Malam/ Yandakan Katsina. Kowannensu Yana hudda da Sokoto Kai tsaye kuma kowa baya shiga huldar kowa, idan Sarkin Sullubawa ya rasu a wancan Lokacin daga Sokoto ne Sarkin Musulmi zai zabi wani ya turo Galadima a nadashi, hakanan ma shima Yandaka idan ya rasu daga Sokoto ne Sarkin Musulmi zai zabi wani ya turo Wakilin shi ayi Nadi a Katsina. Wannan yana daya daga cikin dangantaka tsakanin Katsina da Sokoto.
Hakanan kuma idan an samu wata matsaya a Katsina, Sarkin Musulmi Yana shiga tsakanin ya kawo sasanci, a Katsina. Misali daga Sokoto Sarkin Musulmi ya bada Umarnin tube Sarkin Katsina Saddiqu, (1835-1844) akan wata matsala data faru, a inda aka nada danuwansa Muhammad Bello, shi Kuma Saddiqu aka tafi dashi Kware, bayan da aka cire daga Sarautar aka kaishi acan yaci gaba da rayuwa. Yanzu haka Kabarin shi na can Kware din. Da dai sauransu.
Haka kuma akwai alaka ta auratayya tsakanin Katsina da Sokoto. Misali 1. Sarkin Katsina Saddiqu( 1835-1844) ya auri Nana Asmau diyar Sarkin Musulmi Abdulrahman Danyan Kasko, 2. Haka kuma, Sarkin Katsina Ibrahim ya auri Khadijatul Kubura diyar Sarkin Musulmi Abubakar Mai Raba, ana Kuma kiransa da Mai Kuturu, itace ta haifi 1. Machika Abdu, 2. Malam Shuaibu 3. Malam Adamu da 4. Hauwau Yar Sarki.
Yanzu aka Kabarin Khadijatul Kubura Yana nan sansanin Yan Sarki dake tsakanin Adoro da Unguwar Yari. Ta rasu acukin shekarar 1910.
3. Hakanan Kuma Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo ya auri diyar Sarkin Musulmi Mai Turare. Itace ta haifi 1. Late Alhaji Aliyu Usman Nagogo ( Danmadami) da kuma 2. Alhaji Sabo Usman Nagogo( Danmadami) da sauransu.
Akwai alakar data faru tsakanin Sokoto da Katsina a lokacin zuwan Turawan mulkin Mallaka acikin shekarar 1903. Lokacin da Yan mulkin Mallaka suka ci Sokoto da Yaki acikin shekarar 1903, Wanda ake cema yakin Giginya, sai Sarkin Musulmi Attahiru Ahmadu na I, ya bada Umarnin ayi gudun hijira zuwa Saudiyya, daga Katsina an samu da daman mutane wadanda suka tafi Sokoto, suka shiga ayarin Sarkin Musulmi domin gudun Hijira, Wanda a bisa hanyarsune , suna a Garin Burmi dake Jihar Gombe ta yanzu, Turawan Mulkin Mallaka suka tarbesu aka sake gwabza wani Yakin Wanda yayi sanadiyyar Shahadar Sarkin Musulmi Attahiru da wasu sauran Musulmi.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.