GATANAN-GATANAN KU: Labarin Darajar Neman Sani
- Katsina City News
- 20 Nov, 2024
- 219
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Akwai wani mutum mai suna Duna wanda yake zaune tare da matarsa, Delu, a wani ƙaramin kauye kusa da garin Koki, inda matar Gizo ke zaune. Sun shafe shekaru suna zaman aure ba tare da samun haihuwa ba. Duk da haka, Duna bai damu ba, amma Delu ta dora dukkan al’amura ga Allah.
Ranar da ba a tsammani ba, Delu ta fahimci cewa ta yi batan wata. Ita da mijinta sun yi murna sosai. Bayan wata tara, Delu ta sauka lafiya ta haifi ɗa namiji. Sati guda bayan haihuwar, sun saka masa suna Maishuni.
Da Maishuni ya girma kaɗan, sai Duna ya ce wa matarsa, "Delu, ya kamata mu tura Maishuni makaranta don ya samu ilimi. Ba za mu ci gaba da rayuwa cikin duhun jahilci ba."
Delu ta ce, "Haka ne, amma ina tsoron kada ya sha wahala a can."
Sai Duna ya kwantar mata da hankali, ya bayyana mata muhimmancin neman ilimi, har ta amince.
Maishuni Ya Tafi Makaranta
Bayan Duna ya shirya, ya ɗauki Maishuni zuwa wani gari mai nisa inda ya kai shi tsangayar wani babban malami. A nan ya yi masa nasiha: "Idan ka dawo gida kana son gane mahaifiyarka, ka yi tambaya. Duk wadda ta ce ita ce mahaifiyarka, ka tambaye ta a inda ta haife ka. Idan ta ce a tsakiyar ɗaki, to ita ce."
Bayan wannan wasiyya, Duna ya koma gida. Amma bai daɗe ba, ya rasu. Wannan lamarin ya saka Delu cikin tsananin damuwa, domin ba ta san garin da aka kai ɗan nata neman ilimi ba.
Dawowar Maishuni Bayan Shekaru 27
Shekaru ashirin da bakwai bayan tafiyarsa, Maishuni ya zama babban malami kuma attajiri. Ya ji ƙwazo na ganin mahaifiyarsa, don haka ya fara neman garinsu. Duk da rashin sanin sunan garin, ya yi bincike har Allah ya kai shi gida.
Da ya shiga garin, sai ya fara rera wakarsa:
"Wace ce mahaifiyata?
Wace ce mahaifiyata?"
Mata da yawa sun fito suna da’awar mahaifiyarsa. Wasu sun ce sun haife shi a kan gadaje, wasu a kan tabarmi, wasu ma a kan zinariya. Duk da haka, ba wadda ta bayar da amsar gaskiya.
Daga ƙarshe, sai Maishuni ya hango wata tsohuwa da ke zaune a ƙasa, fuskar ta cike da ƙunci. Ya tambaye ta:
"Wace ce mahaifiyata?
Wace ce mahaifiyata?"
Sai tsohuwar, wadda ita ce Delu, ta yi murmushi, ta amsa da cewa:
"Ni ce mahaifiyarka,
Ni ce mahaifiyarka."
Maishuni ya ce:
"Ina kika haife ni?"
Ta amsa cikin nutsuwa:
"Na haife ka a tsakar ɗaki,
Na haife ka a tsakar ɗaki."
Da wannan amsa, farin ciki ya cika zuciyar Maishuni. Ya durƙusa gaban mahaifiyarsa, yana cewa:
"Lallai ke ce mahaifiyata,
Lallai ke ce mahaifiyata."
Gina Gida da Makaranta
Maishuni ya nemi izinin mahaifiyarsa ya gina mata katafaren gida. Haka kuma ya tara kuɗi ya cika mata tukwane da ɗan ƙaramin rumbu. Bayan haka, ya gina makaranta a garin, inda ya zama babban malami da ake zuwa neman ilimi daga ko’ina.
Darussa Daga Labarin
1. Ilimi shine gishirin rayuwa, kuma tushen alheri.
2. Hakuri yana kawo riba.
3. Ƙaddara ta riga fata.
4. Arziki yana buƙatar ƙoƙari don a same shi.
5. Rayuwa cikin ilimi da son gaskiya tana kawo nasara.
Mun Ciro wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman