KIWON LAFIYA: CUTAR CIWON SUKARI (DIABETES)
- Katsina City News
- 19 Nov, 2024
- 30
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Ciwon suga ya zama daya daga cikin manyan cututtuka da suka fi addabar mutane a halin yanzu. Yawanci, yana shafar masu yawan cin abincin mai sa karfin jiki kamar tuwo, dankali, doya, gari, da makamantansu.
21.1 Abubuwan da ke Haddasa Ciwon Sukari
Duk da cewa har yanzu ba a gano takamammen abin da ke haddasa ciwon suga ba, akwai wasu dalilai da bincike ya nuna cewa suna taimakawa wajen haifar da wannan cuta. Ga wasu daga cikinsu:
1. Rashin wadatar sinadarin *insulin* da matsarmama (*pancreas*) ke samarwa, wanda yake narkar da abincin mai karfin jiki a cikin jini.
2. Yawan cin abinci mai dauke da sinadaran karfi kamar tuwo, dankali, da garin rogo.
3. Gado – ana iya gadar wannan ciwo daga
iyaye.
4. Shekaru – mutane masu shekaru sama da arba’in (40) suna da yawan kamuwa da wannan ciwo.
5. Juna biyu – mata masu ciki suna iya kamuwa.
21.2 Yadda Ciwon Ke Kasancewa
Rashin wadatar sinadarin insulin yana hana sukari shiga cikin kwayoyin halitta (cells) na jini, wanda hakan ke haddasa yawan sukari a cikin jini da fitsari. Wannan yanayi na iya kawo:
1. Ramewa da saurin jin yunwa.
2. Yawan cin abinci fiye da kima.
3. Ciwon fata kamar kyasfi da makero, wanda ba sa warkewa cikin lokaci.
21.3 Alamomin Ciwon Sukari
Ga alamomin farko na ciwon suga:
1. Yawan fitsari mai yawa.
2. Jin gajiya.
3. Jin yunwa akai-akai.
4. Yawan jin kishirwa.
5. Ramewar jiki.
6. Kaikayin fata ko al’aura (musamman ga mata, suna iya samun kaikayi ko ruwa mai wari).
7. Idan ciwon ya tsananta, mutum zai iya shiga hali na rashin sani (*diabetic coma*).
8. Idanuwa su yi kore-kore ko samun kaluluwa a wurare kamar kugu.
Hanyar Ganin Ciwon Sukari
A asibiti ne kawai za a tabbatar da ciwon ta hanyar auna jini ko fitsari. Duk da haka, yana da kyau a guji dandana fitsari, musamman idan mutum yana dauke da cutar AIDS don guje wa daukar kwayoyin cuta.
21.4 Maganin Ciwon Sukari
1. Ga Matasa: Ana amfani da allurar "insulin" don daidaita sinadarin sukari a jiki.
2. Ga Manyan Shekaru: Ana iya rage matsalar ta hanyar cin abinci mai kyau kamar:
- Abincin hatsi kamar gero, alkama, ko acca.
- Wake, kifi, nama, ko zogale.
- Rage nauyin jiki don gujewa kiba.
3. Shan ruwan jan zobo – kofi daya da rabi, sau uku a rana kafin cin abinci.
Matakan Kariya
- Kula da tsaftar jiki da wanke baki bayan cin abinci.
- Guje wa tafiya ba takalmi don kare kafafu daga raunuka.
- Kula da tsabtar tufafi da muhalli.
Daga littafin "Kula Da Lafiya" Na Safiya Ya’u Yemal.