Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima Ya Kaddamar da Shirin Grand Challenges Domin Inganta Lafiya

top-news

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya kaddamar da shirin *Grand Challenges Nigeria* (GCNg), wani shiri na ƙasa da nufin inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar samar da mafita daga cikin gida.  

An gudanar da taron kaddamarwar a Dakin Taro na Banquet da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja. A matakin farko, shirin zai mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara.  

Da yake jawabi a taron, Mataimakin Shugaban ya bayyana cewa an samar da wannan shiri ne saboda gaggawar da ke tattare da saurin ci gaban kimiyya da fasaha a duniya. Ya kara da cewa wannan yana daga cikin manyan muradun gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.  

“Wannan shiri ba kawai don warware matsaloli ba ne, amma wata kafa ce da za ta tallafa wa bincike na zamani, gina ƙwararrun masana, ƙarfafa haɗin gwiwa, da kuma tsara mafita masu dacewa da al’adunmu tare da haɗin kan al’umma,” in ji Shettima.  

Ya kuma tabbatar da cewa shirin GCNg ya nuna jajircewar gwamnatin Najeriya wajen amfani da fasaha don cimma cigaban ƙasa.  

Photo: VP Shettima