Daga Legas ake nema ai mana mulkin-mallaka da katsalandan a harkokin masarautar mu - Kwankwaso
- Katsina City News
- 18 Nov, 2024
- 55
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoan jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce daga ɓangaren Legas a ke yunƙurin mamaye wasu sassa na ƙasar, musamman Kano.
Kwankwaso ya yi ikirarin cewa Legos na tsoma baki a harkokin cikin gida na Kano, musamman masarautar Kano.
Ya bayyana waɗannan zarge-zargen ne yayin jawabi a bikin yaye daliban Jami’ar Skyline da ke Kano a jiya Lahadi.
Da ya ke nuna damuwarsa kan abin da ya kira yin katsalandan, Kwankwaso ya yi gargadi kan matakan da za su iya tauye 'yancin kai da al'adun gargajiya na sauran jihohi.
"Yau, muna ganin a fili akwai gagarumin yunƙuri daga ɓangaren Legas na neman mallakar wannan yanki. Legos ba za ta bari mu zaɓi Sarkinmu ba; a maimakon haka, suna son kakaba mana Sarkinsu a Kano," in ji shi.