FOMWAN Ta Bukaci Hadin Gwiwa da Hisbah Wajen Ayyukan Taimakon Al’umma A jihar Katsina
- Katsina City News
- 15 Nov, 2024
- 222
A ranar Talata, 12 ga Nuwamba 2024, Kungiyar Mata Musulmi wato "Federation of Muslim Women’s Associations in Nigeria (FOMWAN), reshen Jihar Katsina, ta kai ziyara Hedikwatar Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina da ke kan Hanyar Jibia a garin Katsina. Ziyarar ta gudana ne domin neman hadin gwiwa tsakanin kungiyar da Hukumar Hisbah wajen gudanar da ayyuka masu amfani ga al’umma.
Shugabar FOMWAN reshen Katsina, Hajiya Wasila Saulawa, ta bayyana cewa ayyukan kungiyar sun yi daidai da wasu daga cikin ayyukan da Hukumar Hisbah ke gudanarwa. Ayyukan sun hada da gyaran tarbiyya, bayar da taimako ga mabukata, sasanta iyalai, da sauran hidimomin al’umma. Ta bayyana cewa kasancewar dukkan membobin kungiyar mata ne, suna fuskantar kalubale wajen gudanar da wasu ayyuka kamar hana ayyukan badala, wanda ya fi dacewa da maza su gudanar. Saboda haka, ta nemi Hukumar Hisbah da ta ba su goyon baya da hadin kai wajen irin wadannan ayyuka, musamman ta hanyar samar da wakilan maza daga hukumar da za su tallafa musu.
A jawabinsa, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Sheikh Aminu Usman Ph.D (Abu Ammar), ya yaba da irin gudunmawar da FOMWAN ke bayarwa wajen hidimtawa al’umma. Ya bayyana cewa tun kafin zamansa Kwamandan Hisbah, ya kasance yana da kyakkyawar alaka da kungiyar, tare da halartar ayyukansu na da’awah a yankin Funtua da sauran wurare. Ya tabbatar wa shugabar kungiyar da sauran membobinta cewa Hukumar Hisbah za ta yi aiki tare da su domin tabbatar da ci gaban al’umma.
Sheikh Aminu Usman ya kara jaddada cewa, duk lokacin da kungiyar ta fuskanci wata matsala a wajen gudanar da ayyukanta, su sanar da hukumar domin samun tallafi da shawarwari. Ya ce hadin kan hukumomin al’umma kamar Hisbah da kungiyoyi masu zaman kansu kamar FOMWAN yana da matukar muhimmanci wajen kawo sauyi mai ma’ana a al’umma.
Kungiyar FOMWAN ta nuna farin cikinta kan wannan tabbacin da aka bayar, tare da fatan cewa hadin gwiwar za ta ba su damar aiwatar da ayyukansu cikin sauki da nasara. Wannan hadin kai na daga cikin matakan da za su taimaka wajen gyaran tarbiyyar al’umma da kawo zaman lafiya a Jihar Katsina.