AFCON: Super Eagles ba za ta daga wa Benin kafa ba - Ekong
- Katsina City News
- 13 Nov, 2024
- 251
Dan wasan baya na Super Eagles, William Ekong, ya sha alwashin cewa ba za a bayar da dama ba kuma ba za a daga kafaa ba yayin da Super Eagles za su kara da Cheetahs na Benin a gobe, a wasan na biyar na neman shiga gasar cin Kofin Afirka ta (AFCON) a rukunin D da za a gudanar a Abidjan.
Dan wasan mai shekaru 31 ya kasance cikin atisaye jiya tare da sauran 'yan wasa 21, yayin da tawagar da kocin Austin Eguavoen ke jagoranta suka fara shirin fafatawa da 'yan wasan Benin.
Tawagar ta fara atisayensu na farko a filin da suka saba na Stade Felix Houphouet-Boigny a gabanin wasan da za su yi da Cheetahs, wadanda tsohon kocin Super Eagles, mai horarwa daga kasar Jamus, Gernot Rohr, ke jagoranta.
Tare da maki 10 daga wasa hudu, tare da kwallaye bakwai da ba su karbi kwallo a raga ba, kuma suna kan gaba a rukuninsu na D, Eagles za su shiga filin Stade Felix Houphouet-Boigny da kwarin gwiwa, wanda kuma ke matsayin fili da suka doke Guinea Bissau, Kamaru, da Angola a gasar cin Kofin Afirka ta 34 a Ivory Coast a farkon wannan shekarar.
Shi ma wannan filin ne inda suka sha kashi da kwallaye biyu da daya a lokacin bazara a hannun Cheetahs (wadanda suka zaɓi Abidjan a matsayin gida saboda rashin filin da CAF ta amince da shi a ƙasarsu) a wani wasa na cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta FIFA 2026, inda suka fara zura kwallo.