Fassarar jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa - da Musulmi a Birnin Riyadh, Saudi Arabiya.
- Katsina City News
- 11 Nov, 2024
- 187
11 ga watan Nuwamba, 2024
Bari in fara da mika godiyata ga Mai Martaba Sarki Salman Bin Abdul-Aziz Al-Saud, mai kula da Masallatan Harami guda biyu, da ya shirya wannan gagarumin taro.
2. Tare da tsantsar girmama nauyin aikida ya rataya akai na na tsaya a gabanku a yau yayin da muke kokarin kawo karshen rikicin Falasdinu da tabbatar da maslahar samar da kasashe biyu. Wannan manufar tana da matuƙar mahimmanci kuma al’amari ne na gaggawa.
3. Rikicin Falasdinu ya dade yana ci gaba da jawo wahalhalu marasa adadi ga mutane da dama. A matsayinmu na wakilan al'umma masu darajanta adalci, mutunci, da kuma ƙimar rayuwar dan Adam, muna da hakkin na mu kawo ƙarshen wannan rikicin.
4. Ba zai wadatar ba in muka tsaya Allah wadai kaɗai. Dole ne duniya ta yi aiki don ganin an kawo karshen ta'addancin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ya ƙi ci yaƙi cinyewa. Babu wata manufa ta siyasa, ko dabarun soji, ko kuma rashin tsaro da ya kamata ya bada damar salwantar da rayukan da ba su ji ba basu gani ba.
5. A cikin tushen ƙa'idodi na tsarin ƙasa da ƙasa, ƙasashe suna da 'yancin kare kansu. Amma a yayin kare kai dole ne a yi la'akari da daidaito da yin sa daidai da tsarin doka, diflomasiya da tsarin gudanarwa na duniya. Ba zai yiwu a hallaka gabaɗayan farar hula ba, da burinsu da makomarsu a ƙoƙarin yin hakan ba.
6. Taimakon jin kai ba gata ba ne, haƙƙin ɗan adam ne. Babu wani mutum ko dan kasa ne, ko wata kabila, ko wani addini, da za a hana shi samun tallafin a lokutan rikici. Dole ne kuma mu tabbatar da cewa ma'aikatan jin kai dake gaba-gaba suna cikin aminci da koshin lafiya don gudanar da aikinsu a Gaza.
Manyan baƙi masu daraja,
7. Samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu, ya kasance wani ginshikin ne na sabunta fata, wanda ke wakiltar hakkokin Isra'ila da Falasdinawa na tabbatar da 'yancin kai da zaman lafiya. Ba batun diflo