"SHUGABA TINUBU YANA BULLO DA HARAJI IRI DABAN-DABAN NE DOMIN SAMUN KUDADEN RAYA KUDU MASO YAMMACIN KASARNAN"
- Katsina City News
- 10 Nov, 2024
- 234
-Daga Farfesa Usman Yusuf
Wani Dattijon Arewa kuma tsohon Babban Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya ce gurfanar da yara kanana a gaban kotu saboda shiga zanga-zangar neman kawo karshen rashin shugabanci na gari (EndBadGovernance), inda ake tuhumar su da laifin cin amanar kasa ya yi matukar shafar kimar Nijeriya a idon duniya.
Ya yi kiran a biya yaran da iyalansu diyyar azabtar da su da sauran wahalhalun da suka.
A wata hira da Vincent Kalu da aka wallafa a Jaridar Saturday Sun ta ranar 9 ga watan Nuwamba, shekarar 2024, Farfesan wanda kwararren likita ne bangaren matsaloli na cikin Jini da Halittar Jinin, da kuma bangaren Dashen Bargo, ya ce Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana wa `yan kasar nan bakar azaba ba `yar kadan ba. Har ila yau ya tabo batun dalilan da suka sa komawa ga gwamnatin yanki ba za ta yi tasiri ba.
_Mene ne ya zo maka a rai a lokacin da ka ga bidiyon yara kananan cikin yunwa an gurfanar da su a gaban kotu ana tuhumarsu da laifin cin amanar kasa?_
Ban ga bidiyon ba, sai da wasu `yan jarida 2 da ban san su ba, suka aiko mun daga can wata uwa duniya Chicago (Cikago) ta kasar Amurka, da Brisbane (Barisbane) ta kasar Australia (Ausitireliya). Suna tambayar ko an kuma satar yara `yan makaranta a Nijeriya ne, kuma ko wadannnan yara an ceto su ne daga hannun `yan fashin daji. Na kuwa shaida musu cewa kokarin da gwamnatinmu ke yi ne na tursasa wa duk wanda ya nuna adawa da tsare-tsarenta, ta hanyar cin zalin `ya`yanmu.
Masu zanga-zanga su fiye da 2000 ne cikinsu har da mata da yara aka kama su a lokacin zanga-zangar ta EndBadGovernanance (kawo karshen rashin mulki na gari) da aka yi a ranar 1-10 wato kwana goma na farkon watan Agustan shekarar nan, wacce ta auku a yawancin jihohin arewacin kasar nan. Lafin wadannan masu zanga-zanga ita ce sun fito su yi aiki da `yancin da tsarin mulki na kasa ya ba su, na gudanar da zanga-zanga da kuma `yancin taruwa. Aka musu kamun- kazar-kuku, aka lullube musu idanu, aka hana su abinci, aka azabtar da su, aka debe su a cikin motar-shiga-ba-biya (Black maria), daga Kano, da Katsina, da Kaduna, da Gwambe, da Jos, aka kai su Abuja.
Aka cunkushe su har da yara `yan kasa da shekara 18 a wuraren tsare mutane na `yan sanda, suka kwashe fiye da kwana 90, sannan aka tarkata su, aka iza keyarsu, aka gurfanar da su a gaban alkalin babbar kotun tarayya ta Abuja. A ranar da aka gurfanar da su a gaban kotu, duk sun kanjame saboda yunwa, cikin jigata da rashin lafiya, wasun su ba sa iya tsayuwa inda suka yanke jiki suka fadi a cikin kotun. Wadannan yara suna bukatar kulawa a sashen kula da cututtukan yara na gaggawa, ba babbar kotun tarayya ba. An tuhume su da laifukan magidanta kamar su cin amanar kasa saboda sun daga tutocin kasar Rasha, da tunzurin a bijire wa gwamnati, da yin kira ga sojoji su kwace mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wadannan tuhume-tuhume da aka yi wa yara kanana na nuna alama baro-baro na gwamnatin mai doki da saurin yanke hukunci, da ke tsoron al`umarta da gaza kare kanta saboda wahalhalun da ta jefa al`umarta a ciki. Aika-aikar da aka yi wawadannan yara rashin imani ne kuma abin kunya da gwamnatin tarayya da cikakken hadin bakin `Yan sandan Nijeriya da bangaren Shari`a suka taru suka aikata.
Shugaban `Yan Sandan Nijeriya (IGP) wanda a karkashin kulawarsa ce wannan abin kunya ya auku, dole ya dauki cikakken alhaki. An ma ji yana cewa yaran da suka yanke jiki suka fadi a cikin kotu, lauyoyin yaran ne suka tsara musu tamkar wasan kwaikwayo, idan an shiga kotu, su yanke jiki su fadi. Wannan kalamai da ke fitowa daga gare shi, ba su dace ba kuma rashin tunani ne. Muna kira a gudanar da cikakken binciken irin rawar da Shugaban `Yan Sandan Nijeriya, da duka wadanda suke da hannu karkashin kulawarsa suka taka.
Shari` a aiki ne mai mutunci kuma duk ma`aikacinta sai da ya yi rantsuwar kare doka da daukaka ta, da yi wa dukkan `yan kasa adalci.
Dole in yaba wa kwarewa da tsayin dakan da lauyoyin wadannan yara suka yi, saboda taimakon wadannan yara.
Bacin nacin da suka yi na sai an kai wadannan mutane gaban kotu bayan tsare su da aka yi ba bisa ka`ida ba fiye da wata uku, da duniya ba ta san komai a game da su ba, kuma haka za su mutu ko su yi ta zama a tsare har abada.
Ina mai kakkausar sukar rashin tunani da rashin tausayi na lauyoyi masu gabatar da tuhuma, da alkalin shari`ar. Ina kira ga Hukumar Ladabtar da Masu Shari`a, ta hukunta su, su duka saboda nuna rashin kwarewar da ta sa mutuncin bangaren shari`a na kasar nan ya fadi kasa warwas a idon duniya.
A karshe gwamnatin Tinubu ta ba da kai bori ya hau, matsin-lamba daga `yan kasa ya tilasta masa yin watsi da duka tuhume-tuhumen tare da sakin su. Da yake masu iya magana suna cewa tabarmar kunya da hauka ake nade ta, sai ga shi an shirya musu wata liyafa a Fadar Shugaban Kasa a matsayin bakin Mataimakin Shugaban Kasa, wanda shi ya mika su ga gwamonin jihohin su, aka debe su a jiragen sama zuwa jihohinsu.
Muna kiran a gudanar da cikakken binciken wadannan abubuwa na ban takaici da kuma kunya, a biya cikakkiyar diyya ga wadanda aka tsaren da iyalansu saboda azabtar da su, da kuma sauran wahalhalun da aka jefa su ciki.
Fatar mu ita ce gwamnatocin jihohi da ta tarayya su koyi darasin cewa mutane ne suke da karfin iko kuma zanga-zanga da `yancin gudanar da taro na `yan kasa, suna da kariya daga kundin tsarin mulki na kasa, kuma ba za a iya rufe bakin jama`a ba.
Babban abu mai muhimmanci shi ne dole gwamnati ta yi wani abu a kan yunwa da ta zama ruwan dare, da wahalhalu da rashin shugabanci na gari da su ne ainihin dalilan da suka haddasa zanga-zangar, domin wanzuwar zaman lafiya a kasar nan.
_Me kake jin zai kasance tunanin da al`umar duniya za ta yi wa Nijeriya a game da shari`ar wadancan yara?_
Duniya tana kallo kamar yadda `yan jarida biyu daga Amurka da Australia (Ausitireliya) suka tintibe ni tun ma kafin in kai ga ganin bidiyon. Nijeriya ta sa hannu a yarjeniyoyi na duniya masu yawan gaske, da suke kare hakkin yara, kuma Tinubu bugu da kari bayan shi ne Shugaban kasarmu, har ila yau shi ne Shugaba na yanzu, na Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS). Nelson Mandela ya taba cewa “Babu bayani ma fi dadin ji a game da rayuwar al`uma, da ya wuce na yadda take tafiyar da `ya`yanta” Ko shakka babu cin zarafi da abin kunyar da aka aikata wa wadannan yara, ko shakka babu ya yi matukar zubar da girman Nijeriya a idon duniya.
_Wata goma sha takwas da hawan Tinubu mulki, ta ya za ka iya auna gwamnatin ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu?_
Babu wani dan Njeriya da ke bukatar a tunatar da shi cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta gana wa dukkan al’umma bakar wahala musamman yawancin marasa karfi da suke cikinmu.
_Gwamnati tana cewa tsare-tsarenta na tattalin arziki sun soma haifar da, da mai ido, wato kyakkyawan sakamako, Me za ka ce a kan wannan?_
Ban san a wacce duniya mukarraban wannan gwamnati suke zaune a cikinta ba, da har suke tunanin cewa wata kwalliya tana biyan kudin sabulu. Wasunmu da suke zaune a Nijeriya ta wannan duniyar mun san ba haka lamarin yake ba. Na sake daga muryata, na kuma sake daga ta ina gargadi ga gwamnati cewa akwai fa yunwa da fushi a dukkan sassan kasar nan. Tabbas komai na iya faruwa idan gwamnati ba ta yi gaggawar daukar matakan saukaka wa al`umar kasa ba.
Amincewar da Shugaba Tinubu ya yi ido rufe da shawarar da Bankin Duniya ya ba shi na ya cire tallafin mai da barin Naira ta nema wa kanta daraja a duniya (karya darajar Naira) a muhimmiyar kasa mai dogaro kamar Nijeriya, ba a ba ta shawara ta gari ba, batar da ita aka yi. Kara tabarbarewar lamarin ma shi ne a kasassabarsa ta kosawa ya dadada wa Kasashen Yammacin Turai, babu wani shiri ko tsari da ya yi domin kawo saukin bakar wahalar da tsare-tsaren nasa marasa kan gado suka haddasa.
Wadannan tsare-tsare na tattalin arziki da aka kai mu aka baro sun haddasa tsadar kayayyaki da ba a taba gani ba a Nijeriya a shekara 28, abinci ya yi tsada da fiye da kashi 40 cikin 100 ya kuma haddasa tashin farashin komai da komai musamman makamashi da magunguna. Miliyoyin `yan Nijeriya sun daina shan magungunan da suka saba sha da ke taimaka musu rayuwa da ya yi sanadiyyar karuwar mace-macen jama`a sanadiyyar cututtukan da za a iya magance su kamar su hawan jini, da ciwon siga.
A yanzu asibitoci sun koma wuraren ganin likita kawai babu magani ko daya, da suka yi sanadiyyar kaurar ma`aikatan lafiya masu yawan gaske zuwa UK (Yuke), da Canada (Kanada), da United States (Amurka).
_Shugaban Kasan ya yi kira ga `yan Nijeriya su kara hakuri tare da sadaukar da kai. Sai dairayuwa ta bushasha da shugabbanni suke ta yi kamar su sayen sabon jirgi na Shugaban Kasa, da tarin ayarin `yan rakiyar Shugaban Kasa, da irin rayuwa ta kawa da `Yan Majalisun Dokoki na Tarayya suke ta yi da dai sauransu. Shin shugabannin suna nuna kyakkyawan misali ne?_
Batun nan ne da ake cewa ka yi abin da na ce ka aikata, amma ba abin da ka ga nake aikatawa ba.
Shugabanni na gari musu kishin kasa, a kowanne lokaci suna shugabanci abin koyi ne musamman idan kasarsu da al`umar kasar suna fama da matsaloli kamar yadda Nijeriya da `yan Nijeriya ke fama. Irin nuna iko da isa, da izza da girman kai da shugabanninmu a matakin jihohi da nagwamnatin tarayya suke nunawa abin kyama ne. A lokacin da kasar ke fama da mafi tabarbarewar tsaro da muka taba gani a rayuwarmu da yunwa da tsare-tsaren Shugaba Tinubu suka haifar mana, wadannan shugabanni suna ta bushasharsu kamar komai yana tafiya daidai-wa-daida.
Ya nuna ba su ma san wahalhalun da a kullum mutane da ke kowanne sashen kasar ke fama da su ba.
_Arewa ta ki amincewa da kudirin dokar Gyara ga Haraji da Tinubu ya aike da shi Majalisun Dokoki na Tarayya. Mene ne abin da yankin ya ki amincewa da shi a cikin kudirin da yadda zai shafi yankin?_
Duka Gwamnonin jihohin Arewa 19 da wasu fitattun Sarakunan Gargajiya sun yi taro kwanan nan a Kaduna tsohuwar Babbar Birnin yankin domin tattauna abubuwa masu yawan gaske da suka shafi yankin. Batun da ya fi daukar hankalin kafofin yada labaru da yada shi, shi ne nuna kin amincewarsu da kudirin dokar haraji da Shugaban Kasa Tinubu ya aike da shi Majalisar Wakilai. Kudirin na da manufar sauya tsarin da ake bi wajen raba Harajin Tamanin Kaya (VAT) da aka tara. Kudirin ya kawo shawarar a ba jihohin da aka tara harajin na VAT a cikinsu kaso mafi tsoka. Abin da hakan yake nufi shi ne, za a cuci jihohin Arewa saboda duka kamfanonin wadannan manyan kamfanoni, gwamnatin jihar Legas za su dinga biya harajin saboda can ne shalkwatocinsu suke, maimakon jihohin da suke gudanar da ayyukansu.
Ina cikakken goyon bayan matsayin da gwamnonin Arewa suka dauka.
Wadanda suka sani sun bayyana cewa wannan haraji naTamanin Kaya wato VAT, haraji ne da ake dorawa a kan abin da aka saya, da ake cire shi take a nan inda ka sayi kaya, ba inda shalkwatar kamfanin take ba. Misali Kamfanin Siminti na Dangote, yana yin simintin ne a jihar Kogi amma yana biyan harajin na VAT da ya karba wajen masu sayen kayansa, ga shalkwatarsa da ke Legas. Duka kamfanonin mai da suke gudanar da aikace-aikacensu a yankunan Neja Delta, suna biyan nasu harajin na VAT ne a Legas ba jihohin da suke gudanar da ayyukansu ba. Wani misalin kuma shi ne duka bankuna da suke samun ribarsu daga duka jihohi 36 har da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda suke gudanar da ayyukansu, sai dai ba sa biyan harajin nasu na VAT ga wadannan jihohi, sai Legas. Haka nan duka kamfanonin sadarwa da suka samun kudadensu a duka sassan kasar nan, sai dai suna biyan harajin VAT ne ga jihar Legas in shalkwatocinsu suke.
Legas ta zama abin da ta zama ne a yau, saboda dinbin jarin Nijeriya da ake ta tsibewa a can, aka gina duka manyan tituna, da gadoji, da teku, da tashohin jiragen sama, da ainihin manyan rukunin gidaje da sauransu. Su kuwa sauran sassan kasar ba sa korafi ko gunaguni da neman a ba su nasu kason da aka samu daga wadannan zuba jari.
Tsare-tsaren tattalin arziki da na haraji na Shugaba Tinubu, da shafa wa idanunsa toka da ya yi yana ta nada `yan kabilarsa mukamai, da yawancin mutane daga Legas da suke shugabantar duka Ma`aikatu, da Hukumomi da Sassan Gwanati inda aka firar da kudade ko kashe su, ana kallonsa a Arewa a matsayin wani shiri da yake yi na kokarin tarkata dukiya da albarkatun tarayya a mayar da su yankin Kudu Maso Yammacin Kasar nan, su kuwa sauran sassan kasar a bar su da kurun bawa. Wannan ba ya tsaya ga babban hadari ne kawai ba, barazana ce ba `yar kadan ba, ga tsaron kasa da hadin kanta.
_Akwai wannan kiraye-kirayen na a bai wa kowanne yanki `yancin cin gashin kansa._
Ban san su wa ke wannan kiraye-kiraye na a ba kowanne yankin `yancin cin gashin kansa ba, awannan lokacin da kasashen da suka san me suke yi, suke duba gaba, wasu `yan siyasa na Nijeriya masu son zuciya da rashin tunani suna batun a koma baya. Abin da suka kasa ganewa shi ne, baya da suke waigawa, ta yi kyau ne saboda an samu shugabanni na gari da suka jagoranci wadannan yankuna. Duka yankunan shugabanni maza da mata masu kishin kasa da suka yi wamutanensu aiki tsakani da Allah ne suka jagorance su. A yanzu kam abin da kamar wuya, saboda shugabanni ne muke da su a yanzu masu son kan su, da suke rike da duka madafun iko a ko`ina cikin fadin kasar, daga kan su sai iyalan su kawai suka sani.
_Wasu masu sharhi a kan lamuran siyasa suna cewa kirkiro da Hukumar Raya Yanki da aka yi wani shiri ne, na tabbatar da gwamnatin yanki, kana da wannan tunani?_
Nijeriya tana da girma kuma da karfi fiye da duk wani munakisa ta wani shugaba da kansa kawai ya sani. A matsayin kasar nan mai dimukradiyya da ke cikin tsarin mulki, babu wani shugaba da zai iya tilasta wa mutane son ransa ba tare da amincewarsu ta hannun wakilansu da suka zaba ba.
Muna sa ido sosai da sosai kan wakilanmu da muka zaba, kuma za mu ci gaba da yin namu kokarin a matsayinmu na `yan kasa wajen ganin mun kare hakkokin jama`armu.
_Mene ne ra`ayinka a game da hukuncin Kotun Koli a game da `yancin cin gashin kai naKananan Hukumomi, wato ba su kudadensu kai tsaye daga gwamnatin tarayya?_
Abu ne da ya kamata a ce an dade da wuce wajen kuma dole in yaba wa Shugaba Tinubu saboda samun goyon bayan doka ta hanyar wannan hukunci da kotun koli ta kasa ta yanke. A ra`ayina kananan hukumomi sun fi muhimmanci da alfanu ga jama`a fiye da gwamnatocin jihohi kogwamnatin tarayya. Gwamnonin sun dade suna ci da gumin kananan hukumomi ta hanyar rike musu kudaden su da ya sa duka kananan hukumomi 774 da ke kasar nan, suka zama je-ka-na-yi-ka ba abin da suke yi sai biyan albashi kawai, ba sa iya tabuka wa al`umarsu komai.
`Yancin cin gashin kai na gwamnatocin kananan hukumomi muhimmin abu ne wajen rage fatara, da rage kaura da mutanen karkara suke yi zuwa birane, rage rashin aikin yi a tsakanin matasa, da magance matsalar tsaro da take addabar kasar nan.
_Akwai korafe-korafe a game da yadda gwamnonin jihohi suke gudanar da zabukan kananan hukumomi. Ta ya kananan hukumomin za su iya aiki da cikakken `yancin cin gashin kan nasu?_
Duka gwamnoni jihohi a `yan kwanakin nan suna ta ribibi ko hanzarin gudanar da zabukan kananan hukuomi domin cimma wa`adin 31 ga watan Oktoba na shekarar nan, da Kotun Koli ta yanke hukuncin daga wannan rana, babu wata jihar da za a sake tura mata kudaden karamar hukuma muddin ba ta da zababbun shugabannin kananan hukumomi.
Abin takaici, babu wata jiha da ta gudanar da zabe na gaskiya. A maimakon hakan abin da muka gani shi ne yi wa `yan kasa fashin `yancinsu na kada kuri`unsu da rana tsaka. Wannan aika-aikar da gwamnoni suka aikata ba alheri ba ne ga dimukradiyyarmu da muka wahala wajen samar da ita.
_Ana ta daina gudanar da kasuwanci, kanana da matsakaitan kasuwanci suna ta mutuwa, ana ci gaba da jefa mutane cikin kangin neman aiki, da dama aikin ba samuwa yake yi ba._
Kwarai kuwa, abu ne mai tsoratarwa cewa tsare-tsaren tattalin arziki na Shugaba Tinubu ba wai sun tsaya ga saba wa muradun jama`a kadai ba ne, har ila yau suna yakar harkokin kasuwanci ne, shi ya sa muke ta ganin kamfanoni suna ta rufewa, masu kasuwanci suna ta barin kasar, su kuma ma`aikatansu ana ta korarsu. Babu wani tattalin arziki, komai karfinsa kuwa da zai iya jure wa cire tallafin mai tashi guda, da tsadar makamashi, da tsadar rayuwa, da kudin ruwa tsugugu da karya darajar Naira a kasar da ta dogara kacokan da shigar da kayayyakin kasashen waje.
Shugaban Kasa Tinubu ya dage sai ya ci gaba da bullo da haraji daban-daban a kasa, irin haraje-harajen da ya dinga amfani da shi wajen mulkin Legas fiye da shekara 20 da ta shude. Ya manta cewa yanzu shekara ce ta 2024, kuma haraji ba yasa tattalin arziki ya bunkasa, sarrafa kayayyaki ne kadai yake bunkasa tattalin arziki. Dora wa `yan kasa harajin da ba za su iya biya ba, abu ne ba mai alfanu ba ga tattalin arziki.
Ainihin babban abin tsoron shi ne abubuwa sannu a hankali za su kai ga tsayawa cik idan ba an dauki matakan gyara cikin gaggawa ba.
_Me ya kamata `yan Nijeriya su yi don tunkarar hakan?_
Iko dai yana hannun jama`a, kuma ya zama dole duka `yan kasa su sa hannu wajen sa shugabanninmu su dinga aikata gaskiya.
Ban taba kasancewa cikin damuwa sosai a game da kasarmu kamar yadda nake ciki a yau ba. Shi ya sa nake ci gaba da yin kira ga dukkan `yan kasa a mike tsaye, a yi magana a kan gwamnatoci da ke zaluntar al`umma.