Sabuwar kungiyar ƴan ta'adda ta Lukurawa sun kashe mutane 15 a Kebbi
- Katsina City News
- 09 Nov, 2024
- 294
Sabuwar kungiyar da aka ake kira da Lakurawa, sun kashe mutane 15 tare da sace fiye da shanu 100 a Mera, Karamar Hukumar Augie ta Jihar Kebbi, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Fitaccen mutum a garin, Alhaji Bashir Isah Mera (Yariman Mera), yayin tabbatar da harin ga jaridar Daily Trust, ya bayyana cewa kungiyar ta kai hari lokacin da mutanen garin ke shirin tafiya Sallar Juma’a kuma suka tafi da fiye da shanu 100.
“Da jin haka, mutanen garin suka taru a cikin daruruwan su, suka bi su zuwa daji don kokarin kwato shanun.
An yi musayar wuta tsakanin mutanen garin da ‘yan bindigan wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 15 sannan biyu daga cikin Lakurawan sun mutu,” in ji shi.
Mera ya kara da cewa Lakurawan suna boyewa a cikin dajin Sokoto inda suke tsara hare-harensu.
“Tun da farko ba su kashe kowa ba, sai dai su kwace shanu su bukaci mai shanu ya biya ‘Zaka’. Wannan yana faruwa kusan wata biyu kenan. Wannan shi ne harin farko da suka kai wanda suka kashe mutane 15 a garinmu,” in ji shi.
Kakakin Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ba a iya samun sa a waya don yin tsokaci a lokacin hada wannan rahoto ba.