Kungiyar 'Yan Jaridu Ta Ƙasa, Reshen Jihar Katsina, Ta Taya Hakimin Ketare Murnar Cikar Shekaru 24 Kan Gadon Sarauta
- Katsina City News
- 05 Nov, 2024
- 256
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba 2024, ne Mai girma Alhaji Usman Bello Kankara (Kanwan Katsina, Hakimin Ketare) ya cika shekaru 24 a saman karagar mulkin masarautar Ketare da ke cikin karamar hukumar Kankara, jihar Katsina. Wannan lokaci na musamman ya samu tasiri sosai a fannin shugabanci, tsare-tsaren ci gaban al’umma, da kuma hidimar al’ummar masarautar.
Kungiyar 'Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Katsina, karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar, Comrade Tukur Hassan Dan'ali, ta gudanar da wata ziyarar musamman domin taya Kanwan Katsina murnar wannan nasara mai tarihi. Sun kuma tattauna tare da shi game da muhimman batutuwan ci gaba da suka shafi masarautar Ketare da kuma jihar Katsina baki ɗaya, musamman a fannin tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma inganta ilimi da kiwon lafiya a yankin.
Da yake tsokaci a lokacin ziyarar, Comrade Tukur Dan'ali ya bayyana irin alakarsa da mai girma Kanwan Katsina tun lokacin da yake wakilin gidan rediyon jihar Katsina a Kankara. Ya ce, "Bana manta lokacin da aka turo ni Katsina domin wakilci a lokacin bikin nadin mai girma Hakimin Ketare. A lokacin, marigayi Sarkin Katsina Kabir Usman ya bayyana cewa an nada Usman Bello Kankara a matsayin Hakimin Ketare amma da sharadin cewa zai ci gaba da hidimar kasa wa al'umma a hukumar Kwastam. Wannan magana ta mai martaba tana da muhimmanci ga al'ummar jihar Katsina," in ji Dan'ali. Ya kuma yi fatan alheri tare da burin cika shekaru 25 kan gadon sarautar, wato bikin Silver Jubilee a shekara mai zuwa.
A yayin da yake maida martani ga wannan ziyara, Alhaji Usman Bello Kankara ya nuna godiyarsa da farin cikinsa bisa ga goyon baya da kungiyar NUJ take nuna masa, musamman a matsayin tsohon ɗan jarida kuma jagoran al'umma. Ya kuma yi bayani kan irin hidimar da ya bayar wa ƙasa ta fuskar aikin sa a hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya (Kwastam), inda ya rike mukamin Comptroller na shiyya, mai kula da yankunan kudu da wasu sassan arewa.
Hakimin Ketare ya kuma bayyana wasu daga cikin muhimman ayyukan ci gaba da ya yi wa masarautarsa da kewaye, musamman a fannin ilimi. Daya daga cikin nasarorin da ya kafa a wannan fanni shine kafa makarantar sakandare ta farko a garin Ketare, wadda marigayi tsohon gwamnan jihar Katsina, Malam Umaru Musa Yar’adua ya samar bayan kiran da Hakimin Ketare ya yi masa a lokacin. Ya ce, “Lokacin da na ziyarci gwamna Yar’adua, na bayyana masa bukatar samar da makarantar sakandare a garin. Da sauri gwamnan ya aiko kwamishinan ilimi wanda ya duba yankin kuma a nan muka bayar da fili aka gina makarantar, wacce ta zama ginshikin ilimi a yankin,” in ji shi.
A shekarun da suka gabata, Alhaji Usman Bello Kankara ya kasance uba ga kungiyar 'yan jaridu ta jihar Katsina, musamman la'akari da kasancewarsa tsohon ɗan jarida a gidan Radiyo Kaduna, kuma babban jami’in hulda da jama’a a hukumar Kwastam. Tare da cika shekaru 24 a kan kujerar Hakimin Ketare, ya nuna yadda jagorancinsa ya yi tasiri a ci gaban al’umma, yana ba da misalai na ayyuka masu ma’ana da ya gudanar, kamar inganta harkokin lafiya, samar da ruwan sha, da kuma hanyoyin da ke rage matsalolin tsaro a yankin.
Hakimin ya yi ritaya daga aikin hukumar Kwastam a shekarar 2017, bayan ya kai babban matsayi na Comptroller. Amma duk da haka, ya ci gaba da hidimtawa al’ummarsa da jajircewa wajen tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a Ketare da kewaye. Wannan murnar cikar shekaru 24 tana zama wata dama ta musamman ga al’umma, domin kara duba irin gudummawar da ya bayar wajen gina al’umma a matsayin hakimi, dan jarida, da kuma jagoran al’umma.