TAKAITACCEN TARIHIN SARKIN KATSINA MUHAMMADU DIKKO DA CI GABAN DA KATSINA TA SAMU A LOKACIN MULKIN SHI.
- Katsina City News
- 29 Oct, 2024
- 301
An haifi Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko a shekarar 1865, zamanin mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Bello (1844-1869). Muhammadu Dikko ya zama Sarki Yana da shekara (41) da haihuwa. Kamin ya zama Sarkin Katsina riki Sarautar Karshi da Danbarhim da Kuma Sarautar Durbin Katsina watau Hakimin Mani. Ita wannan Sarauta ta Durbi ta samo asaline tun zamanin Dubti- Takusheyi. A lokacin Durbawa suka fara Sarauta a wannan Gari. To, daga nanne sunan Durbi ya fara a mulkin Katsina Baki daya. Koda Durbawa suka yi Kaura su ka koma Birnin Katsina, Sai aka bar Sarautar Dutbi da sunanta na asali Amma maimakon Durbi Sai ta zama Durbin Katsina, Kuma Hakimin Mani. Wadanda suka rike wannan Sarauta sun hada da:
1. Durbi Saddiqu( Badallaje). 1810-1835
2. Durbi Fandiku ( Badallaje) 1836-1860) ( Badallaje)
3. Durbi Gidado 1860-1883( Basullube) Mahaifin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko
4. Durbi Yero 1883-1888( Badallaje)
5. Durbi Sada 1888-1891( Basullube).
6. Durbi Dikko 1891-1906( Basullube) da sauransu.
Sarki Dikko Yana da Mukamin Durbi ne likkafarsa tayi gaba, ya zama Sarkin Katsina.
Dalilin Hawan Dikko Sarautar Katsina Yana da nasaba da zuwan Turawan Mulkin Mallaka Kasar Katsina. Turawan Mulkin Mallaka sun zo Katsina a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 1903 a lokacin Sarkin Katsina Abubakar shine Sarki. A lokacin Sarki Dikko Yana Durbin Katsina, lokacin da Turawa suka zo Katsina an tarbesu ta Kofar Yandaka, sannan aka sabkar dasu a Gidan Yarima dake Unguwar Yarima Katsina. Tun daga wannan lokacinne Sarkin Katsina Abubakar ya hada su da Sarki Dikko, yace Durbi ga Turawa Nan Kaine kibar su Kaine ranar su. Duk abin suke nema su biyo ta hannunka. Sarki Dikko ya zam Lieson Officer tsakanin Turawa da Sarkin Katsina. Acikin shekarar 1905 ne Turawan Mulkin Mallaka suka tube Sarki Abubakar daga Sarautar Katsina Sai suka nada kawun shi watau Malam Yero. Shima Yeron acikin shekarar 1906 Turawa suka cireshi. Sai suka ba Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Durbi Muhammadu Dikko yaci Sarautar Katsina a shekarar 1906, a zamanin Gwamna Lugga. Amma Sir Willion Wallace ne yayi bukin nadinsa a ranar 20 ga Janairu 1907, wannnan shine ya kawo karshen mulkin Sarakunan Dallazawa a Katsina, sannan Kuma yayi Sanadiyyar Hawan Fulani Sullubawa Sarautar Katsina, Wanda har ya zuwa yanzu sune suke Sarautar Katsina.
KADAN DAGA CI GABAN DA KATSINA TA SAMU A LOKACIN MULKIN SARKI DIKKO SUN HADA DA.
1. A lokacin mulkin Sarki Dikko ne aka bude Makarantar Hada Magani ta farko a Arewacin Nigeria a Katsina (Pharmacy School da ake Kira Medical Class.
2. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shine Sarki na farko a Nigeria ta Arewa daya fara kai ziyara Ingila a shekarar 1921 sannan Kuma shine Sarki na farko daya tafi aikin Hajji a shekarar 1921.
3. A Katsina aka cibiyar kula da kiwon dabbobin ta Arewa, wadda aka kafa a Kauyen Modoji a shekarar 1919.
4. Kwalejin farko ta Arewa an Gina ta a lokacin Sarki Dikko a shekarar 1921, an budeta a shekarar 1922. Daliban wannan kwalejin sun hada da 1. Sardsunan Sokoto Kuma Firimiyan Jihar Arewa, 2. Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo, 3. Musa Yaradu, 4. Alhaji Isah Kaita Wazirin Katsina 5. Alh. Abubakar Tafawa Balewa da sauransu.
4. An bude Baitil Mali na farko a Arewacin Nigeria a Katsina ( First Treasurer) a lokacin Sarki Dikko a shekarar 1907.
5. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya Gina Babban Masallacin Jumaa a Katsina a lokacin mulkin shi a shekarar 1937. Wanda kenan Kofar soro, Wanda yanzu akema lakabi da Muhammad Dikko Mosques.
Da sauransu.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.