KADAN DAGA CIKIN DALILAN DA SUKA SA TURAWAN MULKIN MALLAKA SUKA CIRE SARKIN KATSINA MALAM YERO DAGA SARAUTAR KATSINA.
- Katsina City News
- 04 Nov, 2024
- 224
Malam Yero shine Sarki na 8 daga cikin Sarakunan Dallazawa da suka yi Sarautar Katsina. An nada Malam Yero Sarkin Katsina a ranar 2 ga watan January, shekarar 1905. Ya zama Sarkin Katsina Yana da kusan shekara (80) da haihuwa.
A lokacin Turawan Mulkin mallakane suke mulki a Katsina, an nada Yero ne bayan Turawa sun tube Sarkin Katsina Abubakar daga Sarauta.
Kadan daga dalilan tube Malam Yero daga Sarauta sun hada da. 1. Haraji 2. Yunkurin Mahadiyya da Kuma. 3. Yakin Satiru.
1. Haraji.
Acikin watan August na shekarar 1906, ne babban Resident na Kano ya umarci mataimakin Resident na Katsina akan ya sanar da Sarki Yero akan sabon Haraji da Gwamnatin Mulkin Mallaka ta kawo a Katsina ( new Taxation scheme). A lokacin da Palmer yake tattatauna batun sabon Harajin tare da Sarki Yero Sai Yero ya sanar dashi cewa wannan bazai yiyuba domin ya sabama kaidar Musulunci, Kuma mutane ba zasu karbeshi ba. Saboda haka Sai Palmer yaci gaba da gudanar da aikin shi na sabon Harajin sannan ya kafa kwamiti daga cikin wasu Hakimman Katsina cewa suci gaba da gudanar da aikin. Sai Malam Yero ya fito fili yayima Hakimman bayani cewa duk Wanda ya yarda da wannan tsarin sabon Harajin to ya kafurta, Kuma shi babu hannun shi a ciki. Wannan Yana daya daga dalilan da Mr. Palmer ya bada report a Kan Yero cewa yayi Masu rashin biyayya Kuma yana kawo zagon Kasa akan mulkin Turawa.
2. YUNKURIN MAHADIYYA.
Yunkurin Mahadiyya Yana daya daga dalilan cire Sarki Yero daga Sarauta. Yan Mahadi sun fito fili suna fada akan mulkin Turawa. Suna Kira akan cewa duk Wanda yayi aiki tare da Turawa to ya kafurta. Yan Mahadiyya sun samu goyon baya ga wasu daga cikin Sarakunan DAULAR Usmaniyya harda Katsina. Wannan Yana daya daga cikin hujjojin da Assistant Resident na Katsina ya bada akan Sarki Yero ( Insurbordination ).
3. TAWAYEN SATIRU ( SATIRU REVOLT).
Yakin Satiru ya faro ne daga cibiyar DAULAR Usmaniyya watau Sokoto. Yunkurin Satiru yayi sanadiyyar mutuwar Turawan Mulkin Mallaka da dama a Satiru. A ranar 10 ga watan February ne a Satiru aka kashe Acting Resident na Sokoto, da wasu Sojojin Turawan Mulkin Mallaka wajen su (27) duk sun rasa rayukansu.
Wannan yunkurin ya jawo rashin biyaya ga Turawan Mulkin Mallaka harda Katsina. A Katsina an Kai Hari a Barilin Sojan Turawa da wasu ofisoshin Yan mulkin Mallaka. Wannan dalilin yasa aka umarci Resident na Katsina cewa su gudu su bar Katsina don su ceci rayuwar su.
Akan wadannan dalilan da wasu suka sa Mr. Palmer ya rubuta report akan Yero zuwa Hedikwata. Acikin watan November shekarar 1906 ne Hedikwatar ta bada umarni a Tube Sarkin Katsina Malam Yero daga Sarauta. Daga nan aka tafi dashi Lokoja a matsayin Dan Gudun Hijira, Yero ya rasu a Lokoja a shekarar 1919.
Alh. Musa Gambo Kofar soro