Dan Majalisar Jihar Katsina Ya Tallafa Da Magunguna a Asibitoci 35 a Karamar Hukumarsa
- Katsina City News
- 31 Oct, 2024
- 84
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Dan Majalisar Wakilai na karamar hukumar Katsina, Honorable Aliyu Abubakar Albaba, ya gudanar da rabon magunguna ga dukkanin asibitoci 35 na karamar hukumar Katsina, domin magance zazzaɓin cizon sauro. Wannan tallafi ya zo ne a kokarin rage yaduwar cutar maleriya a cikin al’umma, musamman ma a lokacin damina.
An kaddamar da wannan shiri a ranar Alhamis a Babbar Asibitin Haihuwa ta Turai Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda manyan baki suka halarta domin maraba da wannan aiki na alheri. Daga cikin wadanda suka halarci taron sun haɗa da wakilin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Jabiru Salisu Tsauri, wanda shine shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina; Kakakin Majalisar Dokokin jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; Kwamishinan Ruwa na jiha, Dr. Bishir Gambo Saulawa; da Kwamishinan Lafiya na jihar, wanda ya samu wakilcin Daraktan Sashen Yakin Da Cutar Maleriya. Hakazalika, Magajin Garin Katsina, Alhaji Aminu Abdulmumini Kabir, ya samu wakilcin Wakilin Kudun Katsina, Abdu Ilyasu. Taron ya samu halartar sauran 'yan siyasa da manyan jami’an gwamnati ciki har da Kwamitin Yakin Neman Zaben Dan Majalisar karkashin jagorancin tsohon shugaban karamar hukumar Katsina, Alhaji Bala Saulawa, da Dantakarar Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Isah Miqdad.
A jawabin da wakilin gwamnan jihar, Alhaji Jabiru Salisu Tsauri, ya gabatar a wajen taron, ya yaba wa kokarin Honorable Aliyu Abubakar Albaba. Ya bayyana cewa, wannan yunkuri na dan majalisar yana daya daga cikin matakan da ake dauka domin tallafawa kokarin gwamnati wajen tabbatar da tsaro da lafiya ga al’ummar jihar Katsina. "Babu abinda gwamnatin jihar Katsina ta fi mayar da hankali a kai irin tsaro da lafiya. Muna alfahari da samar da cibiyar kula da masu ciwon koda, wanda ya zama cibiyar da ba a yi irinta ba a daukacin yankin Afrika ta Yamma," inji shi.
Haka kuma, Kakakin Majalisar Dokokin jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, ya bayyana cewa Honorable Aliyu Abubakar Albaba ya tsayu wajen yin ayyukan alheri ga talakawa. Ya ce, "Albaba ya ciri tuta wajen ayyukan da suke zuwa kai tsaye ga talakawa. Mun shaida yadda ya kasance abokin huldar talakawa, mai tsayawa tsayin daka wajen taimakon al’umma."
Bugu da kari, a wannan rabon magunguna, an tabbatar da cewa asibitoci 35 na karamar hukumar Katsina sun samu magunguna kamar yadda bukatunsu suke, an kuma samar da kayan tsafta, ciki har da katan-katan na Omo da Hypo don tsaftace muhalli, wanda tsohon Kwamishinan Kasa da Tsaro, Alhaji Usman Nadada, ya bayar domin tabbatar da tsaftar asibitocin.
Wannan aiki ya zama abin alfahari a cikin al’ummar Katsina, musamman ma domin ya kasance hanya mai tasiri wajen bunkasa kiwon lafiyar al’ummar jihar, tare da sanya kwarin guiwa ga shugabanni da su rika yin irin wannan aiki na tallafawa.