Kamfanin Space and Dimension Zai Gyara Filin Wasa na Umar Faruk Umar a Daura
- Katsina City News
- 28 Oct, 2024
- 167
Shararren kamfanin gina filayen wasanni, "Space and Dimension Company Ltd," ya karɓi kwangilar gyara da ƙara darajar filin wasa na Umar Faruk Umar da ke garin Daura, cikin ƙaramar hukumar Daura.
A ranar Litinin, 28 ga Oktoba, 2024, shugaban kamfanin, Injiniya Abukasim Yusuf Sada, ya karɓi filin wasan a Daura domin fara aikin gyaran.
Gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda, ta bayar da wannan aikin don haɓaka harkokin wasanni a jihar. Babban sakataren ma’aikatar matasa da wasanni na jihar, Alhaji Muhammad Rabi’u Muhammad, ya miƙa filin ga mai aikin a madadin gwamnati.
A yayin miƙa filin, babban sakataren ya bayyana cewa gyaran filin wasa ya kasance cikin shirin Gwamna Dikko Umar Radda na inganta harkokin wasanni da kuma ba da dama ga matasa a jihar.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar Daura, musamman matasa, da su bai wa kamfanin haɗin kai da goyon baya don ganin aikin ya kammala cikin lokaci, wanda aka tsara zai ɗauki tsawon makonni takwas.
Mataimaki na musamman ga Gwamna kan harkokin wasanni, Hon. Ahmed Abubakar Adidas, ya bayyana farin cikinsa kan wannan aikin da Gwamna ya bayar don gyara filin wasa.
Shima shugaban kamfanin, Injiniya Abukasim Yusuf Sada, ya gode wa gwamnatin jihar bisa amincewa da kamfaninsa. Ya ba da tabbacin cewa kamfanin zai yi aiki mai kyau da inganci, sannan ya nemi haɗin kai daga al’umma.
A nasa jawabin, ɗaya daga cikin masu shirya gasar wasanni a shiyyar Daura, Alhaji Sani Maye Daura, ya gode wa Gwamna bisa umurnin gyaran filin wasa, yana mai yabawa kamfanin "Space and Dimension Company Ltd." da aka ba kwangilar, bisa ƙwarewarsa wajen gina filayen wasa a ƙasar nan, yana mai fatan a yi aiki mai ɗorewa da amfani ga al’umma.