KASSAROTA Ta Yi Kira Ga Jama’ar Katsina Su Kiyaye Tsaftar Tituna Da Bin Dokokin Hanya
- Katsina City News
- 28 Oct, 2024
- 437
Hukumar Kula da Hanyoyin jihar Katsina (KASSAROTA), ta yi kira ga masu amfani da titunan jihar Katsina da su guji zuba shara ko ƙasa, yashi ko sauran tarkace a kan hanyoyi. Wannan kiran ya zo ne domin rage haɗura da kuma tabbatar da tsaftar titunan jihar Katsina.
Jami’in hulda da jama’a na KASSAROTA, Abubakar Marwana Kofar Sauri, ne ya bayyana wannan sanarwar, inda ya jaddada muhimmancin bin ka’idojin hanya domin samar da yanayin hanya mai inganci da tsaro. Babban Darakta na hukumar, Manjo Rimi (mai ritaya), ya yi kira ga wadanda ke wanke babura, keke napep, da motoci a kan tituna, da su daina wannan aiki, duba da cewa ya ci karo da dokoki masu inganta tsaron hanya.
Haka kuma, Babban Daraktan ya ja hankalin masu sayar da kayayyaki a gefen hanya da kan tituna su daina sanya kaya a inda mutane da motoci suke wucewa, domin ainihin wuraren sun kasance ne domin zirga-zirgar jama’a da ababen hawa.
Manjo Rimi ya roki jama’ar Katsina, musamman masu ababen hawa, da su ba da hadin kai ga KASSAROTA ta hanyar bin dokokinta. Ya tabbatar da cewa ma’aikatan hukumar sun kuduri aniyar aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata da kuma kare martabar hukumar.
Ya kuma gode wa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, bisa goyon bayansa ga hukumar da kuma jama’ar jihar bisa hadin kai da suke ba wa hukumar.
A ƙarshe, Manjo Rimi ya gargadi duk wanda ya karya dokokin KASSAROTA zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada, yana mai tabbatar da jajircewar hukumar wajen tabbatar da tsaron hanya a fadin jihar.