TCN Ta Bayyana Matakan Gyaran Wutar Lantarki a Arewa Bisa Barazanar Tsaro
- Katsina City News
- 27 Oct, 2024
- 347
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya karyata rahotannin da ke nuni da cewa za a dauki lokaci mai tsawo kafin a dawo da wutar lantarki a wasu yankunan Arewa, kamar yadda aka ce ya fito daga bakin Daraktan Tsare-tsaren Samar da Wuta, Injiniya (Hajiya) Nafisatu Ali. A wani taron sauraron jama’a da aka gudanar kwanan nan, TCN ta bayyana cewa tana aiki tukuru domin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta.
Injiniya (Hajiya) Nafisatu Ali, ta bayyana a wurin taron cewa layin wutar Shiroro-Kaduna, wanda yake isar da wutar lantarki zuwa Arewa, ya fuskanci ta’addanci daga ’yan ta’adda. Don haka, TCN ta hada kai da ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro domin tabbatar da tsaron yankin, domin injiniyoyinta su samu damar yin aikin gyaran cikin kwanciyar hankali.
Injiniya Ali ta jaddada cewa tura injiniyoyi ba tare da tsaro ba ba zai yiwu ba, saboda hatsarin da ke tattare da yankin. Ta kuma karyata ra'ayin da ke cewa za a dauki lokaci kafin a dawo da wutar, tare da jaddada cewa TCN na kokarin tabbatar da isar wutar lantarki yadda ya kamata ga dukkanin fadin Najeriya.
Rashin wutar lantarki da yankunan Arewa ke fuskanta yanzu yana da nasaba da lalacewar layin wutar Shiroro-Mando, wanda ya kasance babbar hanyar isar da wuta ga yankin. Rashin tsaro a yankin ya jinkirta aikin gyara domin dawo da wutar.
A matsayin matakin wucin gadi, TCN ta sauya hanyar wutar ta layin Ugwuaji-Apir 330kV, wanda shi ma ya samu matsala kwanan nan.
TCN ta bayyana cewa tana aiki tare da ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA) domin ganin injiniyoyinta sun samu damar shiga yankin da aka yi ta’addanci domin gyara. Wannan matakin yana da muhimmanci wajen kare lafiyar jama’a yayin aikin gyara.
Kamfanin TCN ya jaddada kudurinsa na ci gaba da magance wadannan kalubale, duba da muhimmancin wutar lantarki ga rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasa, tare da damuwar da rashin wutar ke haifarwa ga gwamnati da jama’a a wuraren da abin ya shafa.
Muna tabbatar da cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen yin duk mai yiwuwa domin magance matsalolin da kuma dawo da wutar lantarki a wuraren da abin ya shafa. Inji ta