Ministan Tsaro ya Umurci Sojojin Saman Najeriya da su Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Arewa Maso Yamma
- Katsina City News
- 26 Oct, 2024
- 225
Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, CON, MNI, ya bayar da umarnin ga sojojin saman Najeriya da su ƙara ƙaimi wajen mamaye sararin samaniya domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a kasar, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Ministan ya bayyana wannan bukata a yayin ziyararsa ga hedikwatar runduna ta 213 da ke Katsina, inda ya ce, "Mun samar da ƙarin kayan aiki kamar ƙananan jiragen kai farmaki da jirage marasa matuƙa domin tallafa muku wajen kawar da ayyukan masu garkuwa da mutane."
Har ila yau, ya jinjina wa sojojin kan ci gaban da suka yi a wajen magance matsalolin tsaro, yana mai cewa, "Shugaban ƙasa ya yaba da cigaban da kuka samar, kuma zai samar muku da dukkan kayan aikin da kuke buƙata tare da inganta walwalarku. Ku kawar da matsalar tsaro, dan Allah ku kawar da ita yanzu."
A cikin jawabin sa ga manyan jami'ai na FOB Zurmi da Gurbi Baure, Minista Badaru ya jinjina musu akan kokarinsu na magance matsalar tsaro, yana mai cewa, "Na gan ku gaba ɗaya kun ɗau haramar aiki."
Ministan ya kuma yaba wa gwamnatocin Jihohin Zamfara da Katsina akan yadda suke mara wa gwamnatin tarayya baya a wajen yaƙi da ta'addanci a yankunan, yana mai cewa, "Na tabbata dukkan sauran Jihohi za su ba da haɗin kai."