Gwamnatin Katsina Ta Bai Wa Kwamitin Kula Da Kwasa-kwasan Kiwon Lafiya Wa’adin Sati Biyu ya Kammala Aikin sa
- Katsina City News
- 26 Oct, 2024
- 616
Auwal Isah (Katsina Times)
Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin musamman don duba kwasa-kwasan makarantu masu zaman kansu da ke koyar da kwasa-kwasan kiwon lafiya a fadin jihar, tare da ba shi wa’adin makonni biyu domin gabatar da rahoto.
Mataimakin gwamnan jihar, Hon. Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da kwamitin a fadar gwamnatin jihar a ranar Juma'a, inda ya ce an kafa kwamitin ne domin magance korafe-korafe daga al’ummar jihar dangane da wasu makarantu da ake zargin suna koyar da kwasa-kwasan ba tare da izinin hukumomin da suka dace ba.
“Gwamnatin jihar ta samu korafe-korafe a kan kwasa-kwasan da ake koyarwa a wasu makarantu ba tare da amincewar hukumomi ba. Saboda haka, mai girma gwamna ya ga dacewar kafa wannan kwamiti domin duba batun da kuma kawo rahoto cikin makonni biyu,” in ji Hon. Faruk Jobe.
An nada Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, Dr. Faisal Umar Kaita, a matsayin shugaban kwamitin, tare da Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya, Alhaji Rabi’u Abba Ruma, Alhaji Abu Sufyan, da Dr. Mu’awuya Aliyu, babban mai binciken kudi na jiha, da kuma wakilin Ofishin Shugaban Ma’aikata na jihar a matsayin membobin kwamitin.
Gwamnatin jihar ta umarci kwamitin da ya mayar da hankali kan abubuwa masu zuwa:
1. Duba dukkan kwasa-kwasan da ake koyarwa don tabbatar da cewa an samu izinin hukumomi a kan duk kwasa-kwasan da ake gabatarwa.
2. Daidaita kwasa-kwasan da ake koyarwa da bukatun da suka dace da jihar.
3. Nazarin kwasa-kwasan da ke karkashin ɓangaren shawara a makarantu, tare da cire waɗanda ba su da izini.
4. Sake duba rahotannin da aka taɓa gabatarwa kan makarantu domin tantance sahihancin aikinsu.
5. Tabbatar da tsarin zaɓen shugabannin makarantu don tabbatar da sahihancin zaɓen da Majalisar Gudanarwa ke yi.
6. Gayyatar membobin majalisar gudanarwa ko ma’aikatan gudanarwa don tattaunawa wajen gudanar da aikin kwamitin.
Kwamitin na da wa’adin makonni biyu kacal domin kammala wannan aiki da kuma gabatar da cikakken rahoto ga gwamnatin jihar Katsina.