KUNGIYAR AFAN TA NISANTA KANTA DAGA BASHIN BOGE GA MANOMA

top-news


Kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN) ta nisanta kanta daga wani shirin ba da rance ga manoma wanda ake tallatawa a kafafen sada zumunta na zamani.

Shafin yanar gizon da ke tallata bashin yana ikirarin cewa Ma'aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya tare da hadin gwiwar Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) da bankunan raya masana'antu su ke daukar nauyin bashin.

Har ila yau shafin yayi ikirarin cewa duk manomin da ya shiga shafin zai samu rancen Naira 550,000 don bunkasa nomansa.

Amma wata sanarwa daga shugaban AFAN na jihar Katsina, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ta ce shirin ba da rancen ba komi bane illa damfara.

“Wannan tallen na ba da rancen Naira 550,000 ga manoma damfara ce, muna kira ga manoman Jihar Katsina da su guji shiga wannan shafin na yanar gizo.

“AFAN ba ta da masaniya game da wani shirin bada rance ga manoma ta yanar gizo, ‘yan damfara ne suka tsara shafin don su damfari manoma su raba su da kudadensu.

“Don haka muna kira ga manoma da kada su fada tarkon 'yan damfara.

“Haka zalika AFAN na amfani da wannan damar don sanar da gwamnati da masu ruwa da tsaki da sauran al’umma cewa kungiyar ba ta da wata alaka da wannan shafin yanar gizon da ke tallata bada rancen,” in ji sanarwar.