Kamfanin TCN A Nijeriya Yayi Nasarar Gano Inda Wutar Arewacin Nijeriya ta Yanke Aikin Zai Fara daga gobe Alhamis
- Katsina City News
- 23 Oct, 2024
- 186
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Wata tawagar jami'an aikin gyaran layin wutar lantarki na kamfanin Transmission Company of Nigeria (TCN) sun gano matsalar da ta haifar da katsewar layin Ugwuaji zuwa Apir mai ƙarfin 330kV Double Circuit, da misalin ƙarfe 5 na yammacin yau a yankin Igumale da ke Jihar Benue.
Matsalar da aka gano tana nisan da'ira ɗaya ne, inda aka samu layin 330kV ya tsinke a cikin dajin rafin Igumale. Bayan gano matsalar, an fara shirye-shiryen kai kayan aiki da abubuwan gyara don fara aikin gaggawa.
Saboda mawuyacin yanayin wurin da matsalar ta faru, TCN na buƙatar tura manyan injuna da kayan aiki daga ofishinta na Enugu zuwa wurin domin fara gyara. Hakanan, ana tura mota mai ɗagawa (Hiab) zuwa Igumale don tabbatar da cewa an gyara layin yadda ya kamata.
A ranar Litinin, 21 ga Oktoba, 2024, layin wutar Ugwuaji zuwa Apir mai nisan kilomita 215 ya samu matsala, wanda ya haddasa katsewar wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da wasu sassan Arewa ta Tsakiya.
Bayan ƙoƙarin da tawagogin farko suka yi ba tare da nasarar gano matsalar ba, an gano ta a yau da yammaci.
TCN ta tabbatar da cewa za ta gaggauta gyaran matsalar cikin lokaci. Muna godiya ga haƙurin gwamnati da masu amfani da wutar lantarki a jihohin da abin ya shafa. Inji TCN