Gwamnatin Katsina Ta Bukaci Asibitoci Masu Zaman Kansu Su Cika Ka'idojin Dokar 1990, ko a Kwace Lasisin su
- Katsina City News
- 23 Oct, 2024
- 251
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, (Katsina Times)
Gwamnatin Jihar Katsina ta bukaci dukkan Asibitoci masu zaman kansu da ke aiki a fadin jihar, su tabbatar sun cika dukkannin ka'idojin da doka ta shimfida. Wannan umarni ya shafi asibitoci masu zaman kansu, cibiyoyin haihuwa, jinyar ido, da cibiyoyin bincike. Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta bayyana cewa dole ne wadannan cibiyoyi su sabunta rijistarsu tare da tabbatar da suna da kayan aiki na zamani, ma’aikata masu kwarewa, da kayan aikin jinya masu inganci.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Musa Adamu, ya jaddada cewa cika waɗannan ƙa'idoji wajibi ne don tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama’a. Ya bayyana cewa cibiyoyin da suka kasa bin wannan doka za a dauki matakin rufe su nan take. A cewarsa, dokar Edict No. 5 na shekarar 1990 wacce ta tsara ka’idojin gudanar da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a Katsina, na ci gaba da aiki sosai, kuma gwamnati ba za ta lamunci rashin bin ka’ida ba.
Kwamishinan ya kara da cewa, kwamitin da ma’aikatar ta kafa zai fara gudanar da cikakken bincike kan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a jihar cikin makonni uku masu zuwa. Ya ce, duk wata cibiya da aka samu tana aiki ba tare da bin sharuɗɗan doka ba za a dauki matakin rufe ta ba tare da bata lokaci ba.
Idan ba'a manta ba, a ranar Litinin, 21 ga Oktoba, gwamnatin Katsina ta ba da umarnin rufe dukkanin cibiyoyin koyar da harkokin lafiya masu zaman kansu tare da kafa kwamitin bincike don tantance wa'danda suka cika Ƙa'idojin da ingantaccen tsari na Hukumomin lafiya.
Mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan cibiyoyin lafiya, Umar Mammada Adamu, ya ce, an dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar jama’a, ganin cewa wasu daga cikin cibiyoyin na gudanar da ayyukan su ba tare da bin Ƙa'idojin da suka dace ba. Yace gwamanti ta dauki wadannan matakai ne domin tabbatar da kare lafiya da rayukan al'ummar jihar Katsina.
Gwamnatin ta yi kira ga dukkan masu cibiyoyin lafiya da su gaggauta cika ka'idojin da aka tanada don kaucewa rufe cibiyoyin su da kuma dakatar da lasisin gudanar da ayyukan su a jihar.