Matsalolin Tsaro Ne ya Shafi Rashin Wutar Lantarki A Arewa -TCN
- Katsina City News
- 22 Oct, 2024
- 204
Katsina Times
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da tsayawar layin wutar lantarki mai karfin 330kV DC, wanda ya jefa yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da wasu sassan Arewa ta Tsakiya cikin duhu.
A wata sanarwa da Ndidi Mbah, Babban Manajan Harkokin Jama’a na TCN, ta fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa layin 330kV Ugwaji–Apir na DC biyu ya samu matsala a ranar Litinin, wanda ya jawo katsewar wuta a yankunan da abin ya shafa.
Mbah ta ce: “Da misalin karfe 4:53 na safe, layin Ugwuaji–Makurdi 330kV na biyu ya tsaya, wanda ya sanya 243MW na wutar da ke kan layin ya koma kan layin daya a kan wannan hanya. Da misalin karfe 4:58 na safe, layin daya shima ya tsaya, wanda ya haifar da asarar jimlar megawatt 468. Kusan karfe 5:15 na safe da karfe 5:17 na safe an yi kokarin dawo da layukan amma duk suka sake tsayawa nan take.”
Ta ce, "A ranar Litinin, an tura tawagogin masu duba layin daga yankin Apir da Enugu domin gano matsalar a cikin tafiyar kilomita 215, inda suka duba kusan turaku 245 na rarraba wuta."
Ta kara da cewa, tawagar masu dubawa daga yankin Enugu ba su samu damar fara aikin ba saboda umarnin zama a gida na ranar 21 da 22 ga Oktoba 2024 a yankin Kudu maso Gabas, wanda ya hana su ci gaba da aikin har da matsalar samun man fetur domin motocin sintiri.
"An shirya tsaro domin taya tawagar ta fara aikin duba matsalar a wannan safiyar," in ji Mbah.
TCN ta ce, an dawo da wutar layin 132kV daga New Haven zuwa Apir, amma layukan 330kV har yanzu ba su dawo aiki ba, wanda hakan ya shafi yankin Arewa gaba daya. Ta kara da cewa, layin TCN Shiroro-Mando shima ba ya aiki saboda matsalar tsaro, wanda ya jawo katsewar wuta a yankin Arewa.
A cewarta, TCN tana yin duk mai yiwuwa domin gano musabbabin wannan matsala domin injiniyoyi su gyara, su dawo da wutar lantarki yadda ya kamata.
"Muna ba da hakuri ga gwamnati da masu amfani da wutar lantarki a dukkan jihohin da abin ya shafa, kuma muna tabbatar muku da cewa duk da yanayin kalu-bale nantsaro, tawagarmu ta ci gaba da aikin jiya cikin dare."
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, a shekarar 2024 kadai, kasar ta fuskanci akalla sau takwas na rushewar wutar lantarki na kasa.