Duk Wanda Ya Ce Ƙara Mulkin Soja da Mulkin Siyasa, Ba Dan Kishin Ƙasa Bane— Muntari Lawal
- Katsina City News
- 21 Oct, 2024
- 304
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A wata hira ta musamman da jaridar Katsina Times, tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina a zamanin Gwamna Aminu Bello Masari, Alhaji Muntari Lawal, ya bayyana cewa duk wanda ya ce ya fi son mulkin soja fiye da dimokuraɗiyya, ba shi da kishin ƙasa. Ya yi wannan tsokaci ne ranar Litinin, a gidansa da ke unguwar GRA, birnin Katsina.
Muntari ya jaddada cewa duk da gaggawar da mutane ke nunawa wajen buƙatar canje-canje daga sabuwar gwamnati, wajibi ne a bai wa gwamnatin damar yin aikinta yadda ya kamata. "Shekarar farko ce fa da 'yan watanni sabuwar gwamnati ke ciki. A lokacin da Gwamnatin APC ta soma aiki, ba'a hanzarta ganin sakamakon ba, don haka babu dalilin ganin gwamnati bata yi abin azo a gani ba a yanzu," inji shi. "don haka kafin a fara ganin sauye-sauyen da mutane ke muradi sai anyi hakuri" yace.
Martani ga Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina
Muntari Lawal ya maida martani kan wasu kalaman tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Dakta Mustapha Inuwa, wanda aka jiyo yana cewa kara mulkin soja da kama karyar mulkin jam'iyyar APC. A cewar Muntari, waɗannan maganganu ba su dace da gaskiya ba, kasancewar jam'iyyar APC itace ta kawo mulki cikin tsari na dimokuraɗiyya. "Mu ne muka kafa APC, kuma mu ne muka tabbatar da cigaban ta har zuwa yanzu. Don haka ba zan iya cewa mulkin soja ya fi ba," inji shi.
Ya ja hankalin jama’a da su yi hakuri, su daina garaje, yana mai tabbatar da cewa akwai kyakkyawar fata ga cigaban Nijeriya idan aka bai wa gwamnati dama ta gudanar da aikinta.
Batun Tsaro a Jihar Katsina
Muntari ya kuma yi tsokaci kan batun tsaro a jihar Katsina, inda ya yaba da ƙoƙarin da tsohuwar gwamnatin jihar karkashin Aminu Bello Masari ta yi, musamman wajen yaƙi da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane. Ya bayyana cewa duk da nasarorin da aka samu, wasu jihohi makwafta sun gaza ba da goyon baya, wanda ya kawo tsaiko ga aikin tsaro.
"Batun tsaro a wannan sabuwar gwamnati zan iya cewa, an yi nasara wajen kashe manyan masu garkuwa da mutane kamar Habibu Sububu, amma matsalar ita ce, idan an dakile wata mafaka sai matsalar ta sake ɓallewa a wani wuri. Saboda haka, sai an samu haɗin kai sosai tsakanin gwamnati ta tarayya da jihohi domin magance wannan matsalar."
Kira Ga Haɗin Kai Don Cigaba
A ƙarshe, Muntari Lawal ya yi kira ga al'umma da su kasance cikin haƙuri da goyon bayan gwamnati, yana mai nuni da cewa haɗin kai ne zai kawo mafita ga matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.