Al'ummar Kofar Durbi Kwanar 'Yan Lemu, Filin Samji, Kofar Sauri Sun Nemi Gwamnatin Katsina Ta Gina Hanya Domin Bunkasa Kasuwanci da Tsaro
- Katsina City News
- 20 Oct, 2024
- 412
Al'ummar Unguwar Kofar Durbi Kwanar 'Yan Lemu, zuwa Kofar Sauri a cikin birnin Katsina, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda, PhD, da ta duba yiyuwar gina titi a yankin domin bunkasa kasuwanci, tsaro, da inganta rayuwar al'umma.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, unguwar Kofar Durbi, wadda ke kusa da Filin Samji, tana da babbar hanya mai fadi da ba ta bukatar rushe ko sayen gidaje domin fadada ta. Saboda haka, suna ganin cewa gina wannan hanya zai taimaka sosai wajen bunkasa kasuwanci da inganta zirga-zirgar ababen hawa a yankin.
"Wannan unguwa tana da fadi sosai, kuma tana cike da matasa masu himma da ke gudanar da sana'o'in kasuwanci. Yin wannan titin zai inganta harkokin kasuwanci tare da samar da saukin zirga-zirga," in ji wani daga cikin shugabannin al'umma.
Hanyar da suka nemi a gyara ta fara daga Kofar Durbi bayan Filin Samji, tana ratsa Kwanar 'Yan Lemu zuwa Kofar Sauri. Mazauna yankin sun yi nuni da cewa, samar da wannan hanyar zai inganta tattalin arzikin yankin da jihar baki ɗaya, ganin yadda al'umma da dama ke dogara da kasuwanci a yankin.
Sun kuma yaba da kokarin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ke yi na gyaran tituna da aiwatar da ayyukan raya kasa, sannan suka yi kira ga gwamnan da ya shigar da yankinsu cikin shirin gyaran birni domin suma su amfana da wannan ci gaba.
"Mun tabbatar cewa gina wannan hanya zai jawo masu zuba jari tare da kara habaka kasuwanci a yankin, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Katsina," in ji wani ɗan kasuwa.
Al'ummar Kofar Durbi suna fatan gwamnatin za ta amsa kiransu cikin gaggawa, domin tabbatar da cewa ci gaban da ake samu a wasu sassan birnin Katsina ya kai gare su, tare da inganta rayuwar jama'a da zaman lafiya.