Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Kwamitin Shiryawa Taron PEBEC Na Yankin Arewa Maso Yamma
- Katsina City News
- 19 Oct, 2024
- 409
Ibrahim Tukur Jikamshi KIPA
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da kwamitin shirya taron tattaunawa na yankin Arewa maso Yamma da zai gudana karkashin Majalisar Inganta Muhalli Kasuwanci (PEBEC) a ranar 15 ga Nuwamba, 2024. Taron wanda za a gudanar a Katsina zai mayar da hankali kan inganta muhalli kasuwanci a yankin ta hanyar tattara muhimman masu ruwa da tsaki.
Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, wanda ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umaru Radda a yayin bikin kaddamarwar, ya jaddada muhimmancin wannan taro mai zuwa. “A madadin Mai Girma Gwamna, ina mai farin cikin kaddamar da wannan kwamitin. Nasarar wannan taro na da matukar muhimmanci ga jihar Katsina da yankin Arewa maso Yamma baki daya, domin zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kasuwanci a yankin,” in ji Faskari.
Kwamitin shirya taron karkashin jagorancin Ibrahim Tukur Jikamshi, Darakta Janar na Hukumar Kula da zuba Jari ta jihar Katsina (KIPA), ya kunshi manyan jami'ai daga fannoni daban-daban ciki har da masana tattalin arziki, shari’a, da kafofin watsa labarai. Cikakken jerin sunayen mambobin kwamitin sun hada da:
Ibrahim Tukur, Shugaban Kwamitin
Khalil Nur Khalil, Mai Bawa Gwamna Shawara Kan Tattalin Arziki, Dr. Ibrahim Ghani, wakilin KASEDA, Mansur Amin, Norfal Ahmad, Darakta Janar, ICT Alhaji Shamsu Ahmad, Darakta Janar, Tsare-Tsare, Nura Adamale, Barrister Bashir Umar, Darakta Janar, a sashin Shari’a, Abbas Sambo, Babban Manajan, Hukumar Tsare-Tsare ta Yankin Katsina, Isa Dauda, Daraktan Tsare-Tsare, Ahmad Abdulmumin, Shugaban MAN reshen Katsina, Sani Rabi’u Jibia, Darakta, Kula da Ma’aikata daga Ofishin Sakataren Gwamnati, wanda zai kasance Sakataren Kwamitin
Faskari ya bayyana wa kwamitin ayyukan da aka dora musu, wanda ya hada da tsara yadda za a gudanar da taron cikin nasara, yin aiki tare da PEBEC don tabbatar da kyakkyawar gudanarwa, da kuma tantance yawan mahalarta taron.
“Tunda lokaci na taron ya kusa, ina kira ga kwamitin da ya dauki wannan aiki da muhimmanci da sadaukarwa. Gwamnatin jiha za ta bayar da duk goyon bayan da ake bukata don ganin an cimma nasara,” in ji Faskari a karshe.
A nasa jawabin, Ibrahim Tukur Jikamshi, Shugaban Kwamitin, ya gode wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa amincewar da aka yi musu da wannan muhimmin aiki. Ya tabbatar da cewa kwamitin zai gudanar da aikin da aka dora musu cikin kwarewa da kulawa.
“Muna godiya da wannan babban amanar da aka dora mana. A madadin kwamitin, muna tabbatarwa da Mai Girma Gwamna da al’ummar jihar Katsina cewa za mu aiwatar da wannan aiki cikin kwarewa,” in ji Jikamshi.
Ya bayyana cewa shirye-shirye sun riga sun fara daga yanzu, kuma mun kuduri aniyar ganin an gudanar da taron a cikin nasara, Mako mai zuwa, za mu gabatar da cikakken rahoto da dukkan takardu ga gwamnatin jiha." Ya bayyana.
Jikamshi ya kuma godewa wakilan PEBEC daga Abuja bisa goyon bayan da suka bayar. "Muna godiya da hadin kai da jagorancin da muka samu daga Abuja, kuma zamu gudanar ayyukan mu a kan lokaci.
Taron PEBEC na yankin Arewa maso Yamma ana sa ran zai zama wata muhimmiyar dama don tattaunawa kan hanyoyin inganta yanayin kasuwanci a yankin, wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da jawo jari zuwa jihar Katsina da sauran yankunan Najeriya.
Gwamnatin jiha da kwamitin sun sake jaddada aniyar su na ganin an gudanar da wannan taro cikin nasara, tare da la'akari da muhimmancin da zai yi wajen cigaban tattalin arzikin yankin.