Yiwuwar Raguwar Farashin Man Fetur: IPMAN Ta Fara Tattaunawa da Matatar Dangote
- Katsina City News
- 14 Oct, 2024
- 268
Daga Auwal Isah, Katsina Times
Akwai yiwuwar farashin man fetur zai ragu, bayan da kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta fara tattaunawa da kamfanin Dangote domin saye da rarraba man fetur kai tsaye daga matatar man Dangote. Wannan na zuwa ne bayan tsoma bakin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NMDPRA), wanda ya kai ga tattaunawa tsakanin mahukuntan IPMAN da matatar man fetur ta Dangote.
Rahotanni daga jaridar *Daily Trust* sun bayyana cewa IPMAN ta tuntubi kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL), inda ta koka kan yadda farashin man da suke samu daga kamfanin NNPCL ya kai har Naira 898 kowace lita. Wannan matsin lamba ya sa kungiyar ta nemi hanyar da za ta saye mai kai tsaye daga matatar Dangote domin rage farashin mai ga ‘yan kasuwar.
Wata majiya daga IPMAN ta bayyana cewa NNPC ta amince da bai wa kungiyar damar siya mai kai tsaye daga hannun matatar Dangote ba tare da bin ta hannun NNPCL ba. Wannan ya biyo bayan matakin da NNPC ta dauka na bai wa dillalan mai damar rarraba man daga matatar mai mai yawan lita 650,000 a kullum. Wannan mataki na da nufin saukaka siyan mai ga 'yan kasuwa da kuma tabbatar da rarraba man cikin sauri.
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ‘yan kasuwar man suna da cikakkiyar damar siyan mai kai tsaye daga matatar Dangote ba tare da tsallake wani tsari ba. Wannan ya kara fito da sabuwar fuskar kasuwar man fetur, inda gwamnati ke neman saukaka wa 'yan kasa wahalhalun da suke fuskanta sakamakon tsadar farashin mai a halin yanzu.
Kawo yanzu dai ba a fitar da cikakken bayani kan ko farashin da IPMAN za ta samu daga Dangote zai kasance mai rahusa idan aka kwatanta da farashin da ake sayarwa a kasuwa ba. Sai dai ana ganin cewa idan tattaunawar ta yi tasiri, za a iya samun rangwamen farashin man fetur a kasuwa, wanda zai kawo sauki ga masu amfani da man fetur a sassa daban-daban na kasar.
A makon da ya gabata ne kamfanin NNPC, wanda shi ne mafi girma a kasuwar mai, ya daidaita farashin man fetur inda ya daga shi daga Naira 855 zuwa Naira 998 kowace lita a Lagos, yayin da a wasu jihohi farashin ya kai sama da Naira 1,000. Wannan karin farashi ya sa 'yan kasuwa ke fatan samun sauki idan suka fara siyan man daga matatar Dangote a farashi mai sauki.
Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa wannan mataki zai iya taimakawa wajen rage hauhawar farashin kaya da kuma samar da kwanciyar hankali a kasuwar mai, musamman idan aka samu nasarar rage farashin man fetur ga ‘yan kasuwa da masu ababen hawa.
Za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari don jin yadda za a kammala tattaunawar tsakanin IPMAN da kamfanin Dangote da kuma yadda wannan zai shafi farashin man fetur a kasa baki daya.