Masu Ruwa da Tsaki na Karamar Hukumar Rimi Sun Gabatar da Sabon Shugaban APC ga Gwamnan Jihar Katsina
- Katsina City News
- 14 Oct, 2024
- 227
A ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya karbi tawagar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga Karamar Hukumar Rimi. Tawagar, karkashin jagorancin Alhaji Salisu Mamman Kadandani, ta gabatar da Sabon Shugaban rikon jam'iyyar, Alhaji Nafi’u Abdullahi Makurda, a ofishin Gwamnan da ke Fadar Gwamnati, Katsina.
Gabatar da sabon shugaba ya biyo bayan rasuwar tsohon shugaban jam’iyyar na karamar hukumar, Alhaji Nasiru Muntari Masabo, wanda ya rasu a makon da ya gabata. Tawagar ta kuma bayyana godiyarta ga Gwamna Radda bisa irin ayyukan alkhairin da yake aiwatarwa a jihar, tare da jinjina masa bisa irin mukaman da ya baiwa al'ummar Karamar Hukumar Rimi, wanda suke ganin ya kawo ci gaba mai ma’ana ga yankin.
A cikin tawagar sun haɗa da Sakataren Gwamna, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, Shugaban Karamar Hukumar Rimi, Malam Nu’uman Rimi, Dan takarar shugaban karamar hukumar, Hon. Muhammad Ali Rimi, Hon. Nasiru Ala Iyatawa, Hon. Mua’azu Lemamu, da sauran jiga-jigan jam’iyyar na yankin.
Wannan ziyara ta kara tabbatar da haɗin kai da goyon bayan da jam’iyyar APC ke da shi a yankin Rimi, tare da jaddada cikakken goyon bayansu ga mulkin Gwamna Radda.