Tsaro a Arewa: CNG Ta Gudanar da Babban Taro a Katsina
- Katsina City News
- 12 Oct, 2024
- 298
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) ta gudanar da babban taro a Katsina, inda aka tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya. Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki, da shugabannin al’umma.
Shugaban kungiyar na ƙasa, Dakta Nastura Ashir Sharif, ya bayyana dalilin zaɓen jihar Katsina don gudanar da wannan taro, yana mai cewa, "A matsayinmu na 'Yan Arewa, mun tattauna tare da jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki don samun shawarwari kan yadda za a magance matsalar tsaro." Ya bayyana cewa kungiyar ta yi nazari tare da jami'an tsaro na ƙasa, ciki har da Sojoji, 'Yansanda, da masu binciken tsaro, don nemo mafita.
Dakta Nastura ya ce, "Muna fatan wannan taro zai haifar da ingantaccen tsarin tsaro a dukkan jihohin arewa." Ya bayyana cewa, an yi nazari kan matsalolin tsaro na shekaru da dama, tare da duba takardun tarihi da aka wallafa tun zamanin mulkin Turawa. Hakan ya nuna cewa akwai bukatar a haɗa kai tsakanin dukkan bangarorin da ke da alhakin tsaro.
Daga cikin shawarorin da aka bayar, akwai bukatar haɗin gwiwa tsakanin shugabannin tsaro, gwamnonin jihohi, sarakuna, malamai, 'yan jarida, da sauran kungiyoyi. Dakta Nastura ya ce, "Tsaro ya kamata ya fara daga gida, ta hanyar hadin gwiwa da al'umma."
A lokacin taron, an bayyana cewa jihar Katsina ta riga ta fara wasu shirin tsaro, ciki har da kwamitin Dattawan jihar da Asusun Tsaro. Dakta Nastura ya bayyana, "Muna son kaddamar da wannan tsari a Katsina saboda ta kasance jagora a tattaunawar tsaro a Najeriya."
Farfesa Sani Abubakar Lugga, masanin harkar sasanci da tsaro, ya bayyana cewa, "Matsalolin da ke haifar da rashin tsaro suna da yawa, kuma yana da kyau mu taru don nemo mafita." Ya yi nuni da cewa taron na nuni da bukatar hada kan al'umma don fuskantar kalubalen tsaro.
Dakta Bala Salisu Zango, Kwamishinan ma'aikatar yada labarai, tarihi da al'adu na jihar Katsina, ya wakilci gwamnatin jihar, inda ya bayyana matakan da aka dauka wajen inganta tsaro da samar da ayyukan yi. Ya ce, "Gwamnatin jihar tana kokarin samar da ingantaccen tsaro da ingantaccen kiwon lafiya ga al'umma."
Taron ya samu halartar manyan baki da kungiyoyi masu yawa, ciki har da Kungiyoyin Miyetti Allah, kungiyoyin matasa, da sauran ƙungiyoyin al’umma. Wannan ya nuna alamar hadin kai a cikin al'umma wajen magance matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya.
A karshe, Dakta Nastura ya jaddada cewa, “Muna fatan wannan taro zai zama mataki na farko wajen kafa sabbin hanyoyin magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.” Wannan taron ya kasance wani muhimmin tsari na hadin kai da tattaunawa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki wajen ganin an inganta tsaro a arewacin Najeriya.