KIWON LAFIYA; Lamoniya (Kangarewar Hakarkari) - Ciwon Huhu Mai Tsanani
- Katsina City News
- 12 Oct, 2024
- 352
Lamoniya wata cuta ce mai tsanani da ke kama huhu, inda take sa shi ya zama kamar dutse saboda matuƙar kumburi. Wannan cuta na sa yin numfashi ya zama mai wuya, ko dai shakar iska ko kuma fitar da ita. Duk wanda ya kamu da wannan cuta na fuskantar matsala, amma yara kanana da tsofaffi su ne suka fi kamuwa da ita. Kwayoyin cuta ne ke haifar da wannan ciwo, kuma wasu abubuwa na iya haddasa aukuwar sa, kamar haka:
1. Lamoniya/Kangarewar Hakarkari.
2. Sanyi.
3. Gurɓatacciyar iska ko wani abu, misali hayaki ko kura.
4. Rashin cin abinci mai gina jiki yadda ya kamata, musamman ga yara kanana.
5. Matsanancin motsa jiki.
### Yadda Cutar Ke Shiga Jikin Dan Adam
Ana shakar wannan cuta ta hanci ko bakin mutum. Sai ta tafi zuwa huhu, inda take sa shi ya kumbura. Kwayoyin cutar sukan haifar da wata guba a cikin huhun, wanda zai hana huhu yin aikinsa yadda ya kamata. A cikin wani ɗan lokaci bayan kamuwa da cutar, zazzaɓi mai tsanani da ciwon kirji sukan biyo baya, musamman idan an yi tari ko an shaƙi iska mai sanyi.
### Nau'in Lamoniya
Lamoniya ta kasu kashi biyu kamar haka:
1. **Lobar Lamoniya**: Wadda ke shafar sashe guda na huhu.
2. **Broncho Lamoniya**: Wadda ke shafar sassa biyu ko fiye, ko duka huhun biyu.
### Alamomin Cutar
Ga alamomin da ake gane wannan cuta da su:
1. Zazzaɓi mai tsanani wanda yake kai zafin jiki tsakanin 39 zuwa 40°C.
2. Matsanancin ciwon kirji, wanda ya fi tsananta idan an yi tari.
3. Tari da rashin fitar da majina daga farko, amma bayan kwana biyu majina za ta fara fitowa.
4. Zai yi wuya mutum ya samu numfashi cikin sauƙi, har ya kai ga rashin sanin inda kansa yake.
### Illolin Cutar
Idan ba a nemi magani cikin gaggawa ba, wannan cuta na iya haifar da matsaloli kamar:
1. Taruwar ruwa a cikin huhu.
2. Ciwon zuciya.
3. Mutuwar wani sashe na huhu ko duka huhun.
4. Matsanancin ƙarancin iska a jiki wanda zai iya jawo mutuwa.
### Yadda Ake Gano Lamoniya
Ana gane cutar lamoniya ta hanyar wadannan hanyoyi:
1. Aune majina a asibiti.
2. Daukar hoton huhu (X-ray).
3. Amfani da na'ura wadda ake jin yadda numfashi ke gudana (stethoscope).
### Kansa Na Huhu
Ita kansar huhu tana faruwa sosai a wurin maza fiye da mata har sau biyar (5x). Haka kuma, tana jawo mutuwa cikin sauri idan ba a yi magani da wuri ba.
Daga karshe, cutar lamoniya na da matuƙar haɗari, musamman ga yara da tsofaffi. Don haka, yana da kyau a hanzarta zuwa asibiti idan an ga alamomin cutar don neman magani. Allah Ya tsare mu daga cutuka, Amin.
Daga Littafin Kula da Lafiya Na Safiya Ya'u Yamel