Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala 10,000 Don Sake Gina Masallaci a Damagaram
- Katsina City News
- 11 Oct, 2024
- 268
Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya bayar da gudunmawar dala 10,000 domin sake gina wani babban masallaci da ya rushe a garin Damagaram na Jamhuriyar Nijar.
Masallacin dai na da dadadden tarihi domin an gina shi tun shekaru 200 da suka wuce.
Gwamna Radda ya bayar da gudunmawar ne ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, wanda ke rike da sarautar ‘Turakin Damagaram’.
Yayin da yake bayyana godiyarsa ga Gwamnan bisa gudunmawar, mai alfarma Sultan na Damagaram, Alhaji Abubakar Sanda Umaru, yace tallafin zai taimaka matuka wajen sake gina madaidaicin.
Ya ce hakan zai kara tabbatar da dadaddiyar alakar da ke tsakanin jihar Katsina da Damagaram wadda ta kai shekaru 500.
A nasa jawabin, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ya shaida wa Sultan Umaru Sanda cewa Gwamna Dikko Radda ya bada gudunmawar ne saboda kishinsa na ci gaban addini da al'ummar Damagaram da Jamhuriyar Nijar.
“Mai Girma Gwamna, Malam Dikko Umar Radda, yana da kishin ci gaban zamantakewa da addini na al’ummar Damagaram da Jamhuriyar Nijar baki daya.
"Kuma Malam Dikko Radda na da kishi na karfafa dankon zumunci tsakanin al'umar jihar Katsina da na Damagaram.
“Wannan masallacin zai taimaka wajen cusa tarbiyyar addinin Musulunci a cikin al’ummarmu, kuma hakan zai taimaka wajen magance matsaloli da dama a cikin al’umma.
“Mu mutane daya ne da turawa suka rabu tsakaninmu, shi ya sa ya kamata mu karfafa alakar da ke tsakanin al’ummarmu kuma munhada kai wajen magance kalubalen da muke fuskanta baki daya,” inji Gwajo-gwajo.