"Za Mu Kawo Kaya Masu Araha Har Gidajen Jama’a," inji Gwamna Radda
- Katsina City News
- 10 Oct, 2024
- 315
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar da Shagunan 'Rumbun Sauki' 38 a Kananan Hukumomi 34
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda PhD, ta sanar da shirin kafa shagunan ‘Rumbun Sauki’ guda 38 a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
Wannan shiri na 'Rumbun Sauki' an bayyana shi ne daga cikin kudurorin da aka cimma a taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 10.
Mashawarci na musamman ga gwamna kan tattalin arzikin karkara, Injiniya Yakubu Nuhu Danja, ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin bude shago guda a kowace karamar hukuma.
Haka zalika, babban birnin jihar Katsina zai sami karin shaguna biyu, yayin da garuruwan Daura da Funtua za su samu shago guda daya kowanne, wanda zai kawo adadin shagunan zuwa 38.
Wannan tsari ya yi la’akari da yawan al’umma da cunkoson jama’a a manyan biranen jihar.
An kafa shagunan 'Rumbin Sauki' ne domin sayar da kayan masarufi da abinci a farashi mai sauki, wanda zai taimaka wa jama’a wajen shawo kan tsadar rayuwa da ake fuskanta.
"Wannan mataki wani yunkuri ne na rage radadin wahalar da al’umma ke fuskanta sakamakon kalubalen tattalin arzikin duniya da tsadar kayan abinci," inji Injiniya Danja.
A wani mataki na nuna jajircewa ga wannan shirin, Gwamna Radda ya kaddamar da shagon 'Kantin Sauki' a Jihar Jigawa a ranar 5 ga Oktoba, 2024.
A yayin ziyarar, gwamnan ya bayyana niyyarsa ta kafa irin wannan shagon a Jihar Katsina, wanda yanzu haka yana cika alkawarin da ya dauka.
Gwamnatin jihar ta sanar da cewa za a tsara yadda za a kafa shagunan a wurare da suka dace a kowace karamar hukuma domin saukaka samun damar zuwa ga dukkan jama’a.
Bugu da kari, akwai shirin fadada wannan tsari zuwa yankunan mazabu 361 na jihar domin kawo saukin tattalin arziki ga kowa.
Gwamna Radda ya jaddada kudurinsa na kawo mafita mai dorewa ga matsalolin tattalin arzikin da al’ummar Jihar Katsina ke fuskanta.
"Ta hanyar kawo kayan masarufi masu araha har kofar gidajen jama’a, gwamnati na fatan rage matsin tattalin arziki ga iyalai da inganta yanayin rayuwa a jihar."