Maulidin Tsohon Hadimin Gwamnatin Katsina: Fitattun Manyan Baki Sun Halarta
- Katsina City News
- 09 Oct, 2024
- 402
Tsohon Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A jiya da daddare, an gudanar da Maulidin gidan tsohon mai taimakawa gwamnan jihar Katsina, Alhaji Abdul'aziz Maituraka, wanda ya saba yi kowacce shekara don tunawa da Mauludin Annabi (S). Maulidin wanda aka gudanar a kofar gidan Alhaji Abdul'aziz Maituraka dake Unguwar Daki Tara a cikin birnin Katsina, ya samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen jihar.
Fitattun manyan bakin da suka halarta a taron, ciki har da tsohon gwamnan jihar Katsina, Malam Aminu Bello Masari, wanda yanzu haka shine shugaban hukumar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu na Nijeriya (TETFUND), da kuma Gwamnan jihar Katsina mai ci, Malam Dikko Umar Radda. Baya ga su, akwai dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Hon. Sani Aliyu Danlami, da tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Bature Masari.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda Ph.D
Taron ya samu halartar manyan malamai daga sassa daban-daban na arewacin Najeriya, ciki har da daga jihohin Kano, Bauchi, Kaduna da wasu yankunan. Shehunnan malaman sun gabatar da jawabai masu cike da ilimi da wa'azantarwa, tare da jaddada muhimmancin soyayya, biyayya, da tsantseni ga Annabi Muhammad (S). Malaman sun yi wa jama’a bayanin daraja da falalar Maulidi tare da fadakarwa kan bin kyawawan koyarwar Manzon Allah (S).
A jawabinsa na maraba, Alhaji Abdul'aziz Maituraka ya nuna godiya ga mahalarta taron, musamman tsohon gwamnan jihar Katsina, Malam Aminu Bello Masari, wanda ya bayyana a matsayin gatansa kuma ginshikin dukkan nasarorin da ya samu. Haka kuma, ya jinjina wa gwamnan mai ci, Malam Dikko Umar Radda, tare da yabawa da irin kokarin gwamnatin sa wajen cigaban al'umma.
An rufe taron da addu'o'in neman zaman lafiya da cigaban jihar Katsina da kasa baki daya, inda mahalarta suka yi godiya bisa irin kyakkyawar alakar dake tsakanin al'umma da shugabanni.