An Kama Kwamandan Rundunar Soji Ta 3 A Kano Saboda Zargin Cin Hanci
- Katsina City News
- 09 Oct, 2024
- 301
Kwamandan Runduna ta 3 a Kano, Birgediya Janar M.A. Sadiq, an kama shi kuma an tsare shi a dakin ajiye masu laifi na ‘yan sandan soji a Abuja sakamakon zargin karkatar da tallafin shinkafa da kuma sayar da kayan aiki na soji, ciki har da janareto da motocin aiki, ga masu sayen ƙarfe a kasuwa.
Majiyoyi masu tushe sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa Babban Hedikwatar Tsaro ta kasa ta raba wa rundunonin soji a fadin kasa tallafin shinkafa domin rabawa sojoji a matsayin Tallafi. An ruwaito cewa an raba tallafin shinkafar sau uku zuwa ga sojojin, bisa la'akari da sunayen da aka tsara.
Sai dai, kamar yadda majiyoyi suka bayyana, Birgediya Janar Sadiq ya raba buhunan shinkafa masu nauyin kilo 5 sau daya ga sojoji, sannan ya sayar da sauran buhunan da aka ba shi.
Baya ga wannan, DAILY NIGERIAN ta gano cewa Birgediya Janar Sadiq ya dauke wasu kayayyaki, ciki har da janareto mai karfin gaske na MIKANO, daga sansanin horaswa na soji a Falgore, Kano, sannan ya sayar da su ga masu sayen ƙarfe a kasuwa.
Wannan jarida ta tabbatar da cewa tuni aka nada tsohon rijistara na Kwalejin Tsaron Najeriya (NDA), Birgediya Janar A.M. Tukur, a matsayin sabon kwamandan rundunar.
“Biyo bayan wannan zarge-zarge, Birgediya Janar Sadiq an tsare shi a dakin ajiye masu laifi kuma yana fuskantar bincike daga sashen musamman na bincike na ‘yan sandan soji a Abuja.
“An fara gayyatar sa zuwa Abuja don amsa tambayoyi, kuma nan take aka ba da umarnin a tsare shi. Akwai karuwar zarge-zarge da ake masa.
“Tuni aka nada Birgediya Janar A.M. Tukur, wanda a baya ya kasance rijistara a Kwalejin Tsaron Najeriya, a matsayin sabon kwamandan rundunar,” inji majiyar.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike a kan lamarin, kuma akwai yiyuwar zai fuskanci shari'a a gaban kotun soji.
Mai magana da yawun rundunar soji, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, bai amsa kiran waya da sakonnin tes da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.