Gwamna Dauda Lawal Ya Nuna Alhini Kan Kashe Dakarun Tsaro a Zamfara
- Katsina City News
- 09 Oct, 2024
- 267
A ranar Talata, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta'aziyya tare da bayyana alhininsa game da harin kwanton ɓauna da 'yan bindiga suka kai wa dakarun 'Community Protection Guards' a yankin Tsafe, wanda ya yi sanadiyyar kashe wasu daga cikin su.
Harin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata, yayin da 'yan bindiga suka kai wa dakarun kwanton ɓauna a shingen binciken ababen hawa da aka kafa a ƙaramar hukumar Tsafe.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau, Gwamna Lawal ya bayyana damuwa da takaici kan wannan mummunan harin. Ya ce 'yan bindigar suna kan hanya guduwa saboda matsin lamba daga jami'an tsaro.
Gwamnan ya yaba wa dakarun tsaro bisa jajircewarsu wajen kare rayukan al'umma, inda ya ce, “Na samu labarin harin kwanton ɓauna da aka kai wa dakarun tsaron mu a ƙaramar hukumar Tsafe, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan jaruman Askarawan Zamfara tara.
"Dakarun da suka rasa rayukan su sun haɗa da: Nasiru Aliyu, Jabiru Hassan, Abdullahi Dangude, Bashar Bawa, Mu’azu Musa, Anas Dahiru, Anas Yakubu, Lawali Yunusa, da wani mutum ɗaya."
Gwamna Lawal ya bayyana cewa harin da aka kai aikin matsorata ne, kuma jami'an tsaro za su ci gaba da fafatawa don murƙushe 'yan bindiga a jihar Zamfara da yankin baki ɗaya.
A ƙarshe, Gwamnan ya miƙa ta'aziyya ga iyalan jaruman da suka rasa rayukan su, tare da addu'ar samun sauƙi ga waɗanda suka ji raunuka. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ba da dukkan tallafin da ya dace ga iyalan mamatan.