Rikici a Hukumar KASSAROTA: Shugaba da Sakataren Hukumar Sun Fara Tuhumar Juna
- Katsina City News
- 08 Oct, 2024
- 847
"Bai bin dokar da ta kafa Kassarota" - Sakataren Hukumar
"Ba shi da takardar da ta kawo shi" - Shugaban Hukumar
Mu’azu Hassan @ Katsina Times
A kwanakin baya, jaridar Katsina Times ta samu wata murya da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda wani da ya ce shi ne sakataren hukumar Kassarota ta jihar Katsina yake magana.
Muryar ta yi wasu manyan zarge-zarge ga shugaban hukumar Kassarota, Manjo Yahaya Muhammed Rimi. Daga cikin zarge-zargen akwai rashin bin ka’idar dokokin hukumar, karkatar da kudin hukumar ta hanyar da ba ta dace ba, da nuna bambanci wajen ladabtar da jami’an hukumar idan sun yi kuskure.
Baya ga haka, sakataren ya kara da zargin cewa shugaban ya kasa gudanar da aikin hukumar yadda ya kamata, inda hakan ya jawo jami'an hukumar ba su samu albashinsu na tsawon watanni.
A cikin muryar da sakataren ke cewa yana da hujjojin da ke tabbatar da zarge-zargen da yake yi, ya yi kira ga duk wanda ke son kalubalantar sa da ya kai shi kotu.
Babban editan jaridar Katsina Times ya samu damar ganawa da sakataren, Sanusi Hayatu Sabuwa, a ofishinsa, inda ya tabbatar da cewa shi ne mai yin muryoyin da suka yadu. Ya ce ya yi hakan ne don a gyara kura-kuran da ke faruwa a hukumar. Sanusi ya tabbatar da cewa yana da hujjojin da suka hada da takardu da bayanan ofishin da za su tabbatar da zarge-zargen da yake yi.
Ya yi kira da a kafa kwamiti mai zaman kansa don bincika yadda shugaban ya yi watsi da wasu dokokin da suka kafa hukumar Kassarota. Ya kuma bayyana cewa akwai matsala a yadda kudaden hukumar ke fita da kuma yadda aka sauya launin kayan jami’an hukumar ba tare da bin doka ba.
Sanusi ya nuna wasu takardu da ya ce sun nuna an yi aringizon kudade, inda wani aiki da ya kamata a kashe naira miliyan daya da dubu dari bakwai, aka rubuta miliyan shida da dubu dari bakwai.
Daya daga cikin zarge-zargen da ya yi shine yadda shugaban hukumar ya zama daya daga cikin masu sa hannu a fitar da kudaden hukumar, wanda ya sabawa dokar da ta kafa Kassarota.
Bayan jin ta bakin sakataren, Katsina Times ta tuntubi shugaban hukumar, Manjo Yahaya Muhammed Rimi, wanda ya musanta dukkan zarge-zargen. Ya ce duk abin da yake yi yana da hujjoji kuma ya samu amincewar manyan ma’aikatan hukumar kafin ya yi.
Shugaban ya kara da cewa sakataren, wanda ke zarge-zargen, sau da dama an ba shi aiki amma ya ki yin su, sannan ya ce bai yi biyayya ga shugabancin hukumar ba.
Wani jami’in Kassarota ya shaida wa jaridar Katsina Times cewa babu wata takardar da ta tabbatar da cewa wanda ke ikirarin shi ne sakataren hukumar, "kawai an turo shi ne ta bakin waya."
Binciken Katsina Times ya tabbatar da cewa shugaban hukumar na daga cikin masu sa hannu a takardun bankin hukumar, wanda ya sabawa dokar da ta kafa Kassarota. Haka kuma, binciken ya gano cewa sauyin launin kayan jami’an hukumar bai dace ba, domin kayan sun yi kama da na dakarun CWG, wanda bai dace jami’ai daban-daban su rika sa kaya iri daya ba.
A karshe, binciken ya nuna cewa duk wani abu da shugaban ke aikatawa sai ya tuntubi wasu jami’an hukumar amma banda sakataren.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Taskar Labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779, 08057777762