Sana’ar kayan nauyi na kawo nakasu ga harkar ilimi a Katsina – SUBEB
- Katsina City News
- 04 Oct, 2024
- 297
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar ilimin firamare ta bai ɗaya (SUBEB) reshen Jihar Katsina ta koka kan yadda sana’ar kayan nauyi ke raunana karatun firamare a jihar.
Shugaban hukumar, Dakta Kabir Magaji ya bayyana hakan a yayin hira da manema labarai da aka yi a ofishinsa.
Ya ce, a duk rana sai ya samu rahoton ɓalle ƙofofin makarantu inda ɓarayi ke ɓaɓɓalle kujeru da tebura domin su cire ƙarafunan su saida wa masu kayan nauyi.
“Ba su ma tsaya nan ba hatta kwanon rufi na azuzzuwan makarantun cirewa suke yi su saida wa masu kayan nauyi.”
Shugaban hukumar ya ce, wannan mugun abu yana taɓa lalitar gwamnatin ba ɗan kaɗan ba wanda tana ƙoƙari wajen inganta tsaro a makarantun firamare da ke faɗin jihar.
Haka kuma Dakta Kabir ya ce, hukumar ta rufe makarantu a ƙananan hukumomi 12 da hare-haren ƴan ta’adda ya shafa.
Amma ya ce, ganin yadda yanayin tsaro ya inganta a jihar, hukumar ta fara shiye-shiryen sake buɗe makarantu 15 a waɗannan yankuna.
Har’ilayau, shugaban hukumar kuma ya sanar da cewa, acikin watanni 14 da zuwan gwamnatin Dikko Raɗɗa, sun ɗauki malaman makarantu fiye da 5,000 wand hakan ya sa yanzu jihar nada malaman firamare 30,000.
Manhaja