Al'ummar Kofar Sauri Sun Jinjinawa Gwamnan Katsina Kan Aikin Fadada Hanyar Kofar Sauri
- Katsina City News
- 03 Oct, 2024
- 474
A ranar 30 ga Satumba, 2024, al'ummar Kofar Sauri sun bayyana gamsuwarsu ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, bisa amincewarsa da aikin fadada babbar hanyar Kofar Sauri. Aikin yana daga rukunin shirin bunkasa tituna da zai inganta kyawun yankin da kuma samar da damar tattalin arziki ga mazauna yankin.
A cikin wata wasika da aka rubuta ga gwamnan, shugabannin yankin sun bayyana cewa aikin yana da muhimmanci wajen kawo ci gaba, tare da raya tsohon titin da ya hada da Kofar Sauri da sauran sassan jihar. An bayyana cewa, wannan aiki zai zamo abin tarihi ga Kofar Sauri.
Sun kuma yi kira ga gwamnan da kada ya saurari masu suka ko korafe-korafe marasa tushe daga wasu 'yan yankin da suke kokarin kawo cikas ga aikin. A cewarsu, mafi yawan mutanen Kofar Sauri suna maraba da aikin fadada titin, tare da goyon baya dari bisa dari.
Hakazalika, wasikar ta nuna cewa al'ummar Kofar Sauri suna tabbatar da goyon bayan su ga kokarin gwamnan wajen inganta jihar, tare da yin addu'a ga Allah SWT ya ba shi ikon ciyar da jihar gaba cikin nasara.
Wadanda suka sanya hannu a wasikar sun hada da shugabannin al'umma da dattawa na yankin Kofar Sauri.