YADDA AIKIN HANYOYIN RUWA NA GWAMNATIN MASARI YA CECI RAYUKA - Binciken Musamman
- Katsina City News
- 02 Oct, 2024
- 365
Shin An Ci Gaba Da Ayyukan A Wannan Gwamnatin?
Mahmood Hassan, Katsina Times
An ce tsawon shekaru, ba a taba ganin damina mai girma kamar ta wannan shekarar ba. Ruwan sama ya yi mummunar barna a jihohi daban-daban, wanda ya haddasa lalacewar gidaje da dukiyoyi. A Katsina, barna ta fi yawa a sanadiyyar rugujewar gidaje sakamakon ruwan sama mai karfi, amma an samu saukin ambaliyar ruwa saboda hanyoyin ruwan da aka gina karkashin gwamnatin da ta gabata.
Kowane shugabanci na gari yana shirya ayyuka don amfanin shekaru masu zuwa, ba don nan da nan ba. Gwamnatin APC ta Aminu Bello Masari ta yi aiki tukuru wajen gina hanyoyin ruwa, wanda ya zama sanadin ceton rayuka a wannan shekarar ta 2024.
A cikin birnin Katsina, kafin wannan lokaci, kowace shekara ana fuskantar ambaliyar ruwa a unguwanni daban-daban, kamar unguwannin da ke bayan filin idi a Kofar Guga. Binciken Katsina Times ya gano cewa akwai manyan hanyoyin ruwa guda biyu da ke kwashe ruwan sama daga cikin birnin Katsina.
Hanya ta farko tana farawa daga bayan FCE har zuwa Kofar Sauri ta bi ta gidan karfe, ta fice zuwa kasar Nijar. Hanya ta biyu tana tasowa daga bayan makarantar polytechnic ta wuce zuwa Kofar Guga, sannan ta hadu da hanya ta farko can wajen Shinkafi.
Ayyukan hanyoyin ruwa sun fara ne tun shekarar 2016 karkashin tallafin gwamnatin tarayya da ta jaha. A shekarar 2020, da hadin gwaiwar bankin duniya, gwamnatin Masari ta fara wani babban shirin mai suna Newmap, wanda ya shafi fadada manyan hanyoyin ruwa daga wajen birnin Katsina zuwa cikin birnin.
Wannan aiki ya kawo saukin ambaliyar ruwa a unguwanni da dama a cikin Katsina, musamman yankunan da ke kusa da wadannan hanyoyin. Babban sakatare a ma’aikatar muhalli na lokacin, Alhaji GeGe, ya tabbatar da cewa gwamnatin jaha ta bayar da goyon baya mai karfi don tabbatar da ingancin aikin.
Haka kuma, irin wadannan ayyukan sun fadada zuwa garin Jibia, wanda ke fama da ambaliyar ruwa mai cin rayuka da dukiya a shekarun baya. Yanzu an samu sauki mai yawa. Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta ci gaba da ayyukan gina hanyoyin ruwa da aka fara karkashin shirin Akresel, wanda ya hada hannu da gwamnatin tarayya, jaha, da bankin duniya.
Wannan cigaba ya taimaka wajen hana Katsina fuskantar matsananciyar ambaliyar ruwa kamar yadda aka gani a wasu jihohi a wannan shekarar.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Taskar Labarai
@ www.taskarlabarai.com
Lambobi: 07043777779, 08057777762