Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Hukumar Gudanarwa Ta Kwalejin Fasaha Da Kere-Kere (KSITM)
- Katsina City News
- 30 Sep, 2024
- 299
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da hukumar Gudanarwa ta Kwalejin Fasaha da Kere-Kere ta Jiha.
An gudanar da taron ƙaddamarwar a Ofishin ma'aikatar Ilimi Me zurfi, Fasaha, da Ilimin Sana'o,i tare da jawabin Kwamishinan ma'akaitar Hon. Isah Muhammad Musa a madadin Gwamnan jihar Katsina, a ranar Litinin 30 ga watan Satumba.
Kwamishinan wanda ya jaddada rawar da majalisar zata taka wajen tabbatar da bin manufofi da fadada damar samun ilimi, musamman ga al'ummomin karkara.
A cikin jawabinsa, Isah Muhammad ya jaddada nadin Dr. Muttaqa Rabe Darma a matsayin shugaban majalisar, inda ya bayyana tabbacin sa kan kwarewar sa da sauran mambobin majalisar. Kwamishinan ya sake nanata mahimmancin bin ka’idojin da aka kafa domin cimma nasarar wannan cibiyar.
Sabbin mambobin majalisar sun samu umarni da su tabbata suna gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, adalci, da bin tsari mai kyau wajen jagorantar wannan cibiya zuwa ga zama cibiyar kirkire-kirkire a fannin fasaha da ilimi.
Kwamishinan ya nanata cewa Kwalejin Fasaha da Kere-Kere tana da muhimmiyar rawar da zata taka wajen habaka makomar matasan jihar ta hanyar ba su ilimi da basirar da za su iya fuskantar kalubalen duniya.
A jawabin sa, shugaban Majalisar Gudanarwa Injiniya Muttaqa Rabe Darma Ya Sha Alwashin Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci
Dr. Muttaqa Rabe Darma, Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin, ya tabbatarwa mahalarta taron cewa majalisar za ta gudanar da ayyukanta cikin kwarewa da adalci. Ya bayyana irin nauyin da ke wuyan majalisar kamar yadda dokar da ta kafa cibiyar ta tanadar, kuma ya yi alkawarin bin tsari da gaskiya a dukkan ayyukan su.
Dr. Darma ya kuma bayyana kudurin majalisar na inganta koyarwa da bincike a cikin cibiyar, tare da burin mayar da ita matsayin babbar cibiyar ilimi a cikin shekara biyu masu zuwa. Ya kammala da jaddada cewa zaman farko na majalisar zai zayyana hanyoyin cimma wannan buri, domin tabbatar da cewa kwalejin ta zama cibiyar ilimi da kirkire-kirkire a yankin.