ALHAJI ATTAHIRU BAFARAWA:GARKUWAR TALAKA
- Katsina City News
- 22 Sep, 2024
- 471
Marigayi Dokta Alhaji Adamu dan Maraya Jos ,Allah ya jikan shi,ya gafarta ma shi.(Maza sun ci kasuwa sun koma) , Wakokinshi na cike da nasiha. A daya daga cikin wakokinshi yai wata waka da ke nuna daidaito tsakanin talaka da mai kudi. (mai akwai da babu) . A cikin wakar ya nuna duk dukiyar mutum,in yana da gida 30 a cikin daya dai zai kwana,a gado daya,a gefen gado daya,kamar wanda keda gida daya. Duk gadarar mai akwai , hula daya zai sa a kanshi. Da agogon jikka talatin da ta sule talatin duk aikin su iri daya ne a bangaren nuna lokaci.
A wata wakar mai taken "Kasa mai cinye-cinye,dan Maraya,ya lissafo wasu attajiran duniya ya fara da dan Karuna zuwa John D. Rockefeller ,Matori Bauchi,Sangon Sarina da sauran su,ya ce ina suke yau?
A wata hikaya,da marigayi Alhaji Abubakar Imam ya bada akan matsolon attajiri da ta Kai har 'ya'yanshi sun dauko hayar wani malami domin yai mai wa'azi,da wa'azi yai wa'azi sai aka ga gogan naku ya fara zubar da hawaye. Sai ko murna ta kama 'ya'yan nan,suka tambayi babansu dalilin da yasa yake kuka. Nan tanke ya amsa masu cewa gemun malamin ne ke tuna ma shi da bunsurunshi da aka sace bara . Nan take 'ya'yan suka fice.
Can baya,attajiri Alhaji Aminu Dantata ya taba shaida ma Kashim Shettima cewa bai jin dadin duniya.
A Najeriya har yanzu in aka ambaci wasu attajira za ka ji ana masu addu'a. Misali ,Galadiman Kano marigayi Tijjani Hashim.
Akwai shugabanni da ake shirya ma lakca duk shekara,misali,sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello,Mallam Aminu Kano,Murtala Muhammad,da sauran su. Labarin marigayi Janaral Hassan Usman Katsina abin sha'awa ce ga matasanmu. Wani ya taba ba ni labari cewa Janaral Hassan Usman Katsina ya taba ba wani takadar kwalin sigari ya ce ya je ya Kai ma wani jami'in gwamnati ya bashi aiki,Kuma da ya Kai aka cika ummarni. Kazalika, a wata hikayar,wata rana Hassan Usman Katsina ya buga ma wani mai kudi waya. Ga yadda hirar ta kaya:
"Hassan ne
"Daga wancan bangaren aka amsa da cewa "ranka ya dade ,Allah ya Kara ma lafiya da tsawoncin kwana"
Hassan: "ba ni da kudi" kawai Hassan ya aje kan tarho.
Wallahi a shedar gani-da-ido, ba ai sa'a guda ba, sai ga kwalaye biyu cike da kudi an kawo falon Janar. Kuma wanda ya turo kudin ya kira tarho shike godiya. Shi da kyauta shi da godiya. Tab da akai mazaje.
Janar Hassan Usman Katsina ya taba tura wani mutum wajen wani cewa ya dauke shi aiki ,wancan ya nuna ba gurbi. Kun San komi Hassan ya ce Mai? " Kai idan aka cire ka za a samu gurbin"? Yo ai nan take sai ahi ,da ban hakuri . "Ranka ya dade tuba ni ke,za a samu gurbi". Dan tselen uwa! Ya hango wahala.
Haka akai da marigayi Tijjani Hashim ,ya tura wani a wani banki ,wancan ya nuna ba gurbi ,Wallahi sai da manajan yabar Kano.
Ba Garkuwar Sakkwato Attahiru Bafarawa ya fara kyaut fara kyautar
NAIRA BILIYAN DAYA BA. Alhaji Aminu Dantata,Dangote,Abdulsamad Isyaka Rabiu sun sha yi. Sai dai bambancin shi ne Bafarawa ya yi wannan kyauta ga talakawa a lokacin da ake bukata,a lokacin da kyauta ke wahala, ba kuma tare da ya ginda wasu sharudda ba.
Dole mu jinjina ma Bafarawa.
Kudi dai a duniya ake nemansu ,Kuma a duniya ake kashe su . Ba a guzurinsu zuwa lahira. Attajirai da yawa suna ci ga ba da gasar tara kudi da boye su,zagaye da su mutane na cikin kogin talauci,Kuma ba su kyauta sai riya ko wadda za su ci riba can gaba.
Allah ya ba mu dukiya irin ta Abubakar Saddiku ba iron ta dan Karuna ba.
DAGA KWAMARED BISHIR DAUDA SABUWAR UNGUWA KATSINA
BABBAN SAKATAREN KUNGIYAR MURYAR TALAKA NA NAJERIYA