Musabakar Alkur'ani Mai Girma Ta Tsauri Foundation Da Aka Gudanar a Katsina: Wani Muhimmin Bangare na Bukukuwan Nadin Lamidon Katsina
- Katsina City News
- 20 Sep, 2024
- 437
Muhammad Aliy Hafiziy, Zaharaddeen Ishaq Abubakar
A yayin shirye-shiryen nadin Hon. Jabiru Tsauri a matsayin Lamidon Katsina da za a gudanar ranar Asabar, 21 ga watan Satumba 2024, an gudanar da gagarumin taron musabakar Alkur'ani mai girma a ranar Alhamis, 19 ga Satumba, 2024. Wannan gasar ta kasance wani muhimmin bangare na bukukuwan nadin, wanda aka shirya domin ƙarfafa ɗalibai akan karatun Alkur'ani a tsakanin matasa da makarantu na jihar Katsina.
Taron ya gudana ne a karkashin jagorancin Lamido Foundation, inda aka gayyaci makarantu guda goma daga sassa daban-daban na jihar don shiga gasar. Makarantun sun fafata ne a cikin wani tsari mai kyau na hizif-hizif, wanda aka tsara don tantance waɗanda suka fi kwarewa a karatun Alkur'ani. Gasar ta samu nasarar jawo hankalin manyan baki, ciki har da shugabannin siyasa, manyan 'yan kasuwa, da kuma shugabannin addini.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Sani Daura, shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji AA Rahamawa, Alhaji Sani Turaki, Alhaji Abubakar Abdullahi Shaisakawa, Mai girma Dan Buran Daura, Alhaji Muhammad, hakimin Baure, da sauran manyan mutane da suka haɗa da Limamin masallacin Bani Coomassie, wanda ya jagoranci addu'o'i da fatan alheri ga ɗaliban da suka halarci gasar.
Shugaban hukumar Hizba ta Jihar Katsina, Dr. Abu Ammar, ya bayyana jin daɗinsa game da yadda aka gudanar da musabakar cikin tsari na addini da ɗa’a. Ya kuma yabawa Hon. Jabiru Tsauri da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban addinin Islama, musamman wajen shirya irin wannan gasa a matsayin wani bangare na bukukuwan nadinsa. Ya ce, "Wannan musabaka ta nuna ƙwazon Hon. Tsauri wajen tallafawa harkokin addini da al’umma."
A cikin jawabinsa, Hon. Jabiru Tsauri ya yi nuni da cewa, shirya wannan gasa yana daga cikin burinsa na ƙarfafa al’amuran addini a Katsina, musamman wajen taimakawa makarantar Alkur’ani da masu karatun Alkur’ani. Ya bayyana cewa zai tattauna da Gwamnan Jihar Katsina don ganin yadda gwamnati za ta ƙara tallafawa waɗannan makarantu domin tabbatar da cigaban karatun Alkur'ani a fadin jihar.
Bayan gasar, Hon. Tsauri, wanda shi ne shugaban ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, ya jagoranci karrama ɗaliban da suka zo na farko a gasar. An ba su kyaututtuka na musamman domin ƙarfafa su wajen cigaba da kokari a karatun Alkur'ani. Haka kuma, ya tabbatar da cewa Tsauri Foundation za ta cigaba da bayar da irin wannan tallafi a dukkan sassan jihar Katsina domin cigaban ilimin addini.
Taron musabakar ya kasance wani muhimmin sashe na bukukuwan nadin Lamidon Katsina, wanda ke kawo haɗin kai da inganta al'amuran addini a cikin al’umma. Taron ya kuma ƙare da addu’o’i na fatan alheri da zaman lafiya a jihar Katsina baki ɗaya.