YADDA BIKIN BADA SANDAR GIRMA YA SAMO ASALI A DAULAR SOKOTO.
- Katsina City News
- 19 Sep, 2024
- 370
Bayan da Turawan mulkin Mallaka suka ci Daular Sokoto da yaki a shekarar 1903, Sai suka bullo da wannan hanya ta shiirya bikin ba Sarki takardar tabbatar da nadinsa da bashi wata Sanda da suka zo da ita daga Kasar Ingila, wadda ake cema Sandar GIRMA. Turawa Kan shiiya irin wannan biki dai dai da al'adar Kasar su, da wadda suka iske anayi nan Kasar. Turawa sun kirkiri wannan biki na bada Sandar GIRMA, don su nuna ma Sarki cewa, akwai na gaba dashi da zai aiki na karkashin shi, watau Rasdan, da DO da Gwamna. Ta hakane suka mulki talakawa ta hanyar Sarakunan su(Indirect rule), kamin a farga Sai aka Taras shugabannin alummma ya koma umarnin Turawa, hatta Shariar musulunci da sannu sannu Saida suka janyeta , suka kawo Finalcot da Constitution da sauransu. Tun daga wannan lokacin ne Turawa suka karbe ikon zartaswa daga hannun Sarakuna, suka Kuma nuna ma sauran shuwagabannin gwamnati Yan Kasa da suyi haka.
Sarkin Musulmi Attahiru na II, shine Turawa suka fara nada shi a matsayin said na shugaban Sarakunan Musulunci na Kasar nan a shekarar 1903, Kuma shine Sarki na farko a Daular Sokoto da Turawan Ingila suka fara bashi Sandar GIRMA.
A Katsina, lokacin da Turawan suka zo a ranar 28-03- 1903, ba a yi fada da Turawa ba. Washe Gari, Sai Turawa suka sake nada Sarki Abubakar na Dallazawa a shekarar 1903, ance Lugard ya an shi Takobin da Korau ya yanka Sanau daga hannun Sarki Abubakar, sannan ya bashi Sandar GIRMA ta Ingila, wannan Yana nuna mulki ya ta shi daga hannun Sarakuna ya koma hannun Turawa. Bayan da Turawa suka tube Sarki Abubakar, Sai suka nada uncle din shi Malam Yero a watan January 1905. Sarki Yero shine Sarki na biyu da Turawa suka sake ba Sandar GIRMA, a Bunfai cikin Kano, ance Lugard yaba Yero Sandar GIRMA sannan Kuma ya maido Takobin Korau ya sake ba Sarki Yero.
Acikin Shekarar 1906 ne Turawa suka tube Sarki Yero, Sai suka ba Sarki Dikko rikon Sarautar a shekarar 1906. Acikin Shekarar 1907 ne Turawa suka tabbatar ma Sarki Dikko da Sarautar Katsina, an ce wani. Baturen Ingila ne Mai suna Mr. W. M Wallace (Acting High Commissioner) shi ne ya ba Sarki Dikko Sandar GIRMA. Daga Sarki Dikko sai dansa Sir Usman Nagogo, Wanda Gwamna Arewa Sir Arthur Richards ya bashi Sandar GIRMA a shekarar 1944. Daga Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo Sai dansa Dr. Muhammadu Kabir Usman, Wanda Governor Kaduna Alhaji Abba Musa Rimi ya bashi Sandar GIRMA a shekarar 1982.
Sai Kuma Sarki na yanzu watau Dr. Abdulmumini Kabir Usman, Wanda Barrister Ibrahim Shehu Shema ya bashi Sandar GIRMA a shekarar 2008.
Abin lura anan shine, Turawan mulkin Mallaka suka kawo wannan al'adar ta ba Sarki Sandar GIRMA, Amma har yanzu tana Nan duk da.cewa Turawa sun bamu yanci.
Musa Gambo Kofar SORO.