Tsarabar Juma'a: Siffofin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW
- Katsina City News
- 08 Sep, 2023
- 787
Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mutum ne da ke da matukar kima da daraja a duniya baki daya musamman ma musulmai wanda ya rayu sama da shekaru dubu da suka shude a garin Makka da Madina, kasar Saudiyya a yanzu. Mabiya addinin musulunci dai sun yi imanin cewa shine annabi na karshe kuma shi ne ya zo da alkur'ani mai girma kuma tsarkakke ne dake da cikakkiyar siffa da kamala wajen jiki da kuma halaye masu kyau.
Ga dai wasu daga cikin siffofin sa nan kamar yadda suka zo a hadissai:
1. Fuskar sa ta daidaita kuma tana da matukar kyaun siffa, Anas Bin Malik ya bayyana fuskar sa da farin wata. A wani kaulin ma yace gaskiya fuskar sa tafi farin wata kyau da kyalli.
2. Manzon Allah SAW dogo ne kuma mai tsayayyen jiki. Ance cikin sa bai turo ba, baya da tumbi.
3. Idanun fiyayyen halitta sun yi matukar halittuwa kuma sun daidaita a fuskar sa. Bakin cikin idon yayi baki sosai, farin idon kuma yayi fari sosai shima.
4. Manzon tsira an ruwaito cewa yana da zazzakar murya kuma yana da dogon wuya wanda yayi daidai da shi.
5. Manzon Allah SAW haka zalika ance fuskar sa cike take da gemu da kuma saje wanda yayi masa matukar kyau.