JAM’IYYAR PDP TA DAKATAR DA SANATA UMAR IBRAHIM TSAURI
- Katsina City News
- 14 Sep, 2024
- 452
Mu'azu Hassan @ Katsina Times
Jam’iyyar PDP a mazabar Tsauri, karamar hukumar Kurfi, ta dakatar da Sanata Umar Ibrahim Tsauri daga jam’iyyar, tare da sanar da uwar jam’iyyar ta jiha.
Katsina Times ta samu kwafin wata takarda da shugaban jam’iyyar PDP na mazabar, Danjume Abubakar, da sakatarensa, Abdullahi Garba, suka sanya wa hannu a ranar Asabar, 13 ga watan Satumba, 2024. Takardar ta tabbatar da aika sakon ga shugaban jam’iyyar ta karamar hukumar Kurfi da kuma uwar jam’iyyar a jihar Katsina.
A cewar takardar, an zargi Sanata Tsauri da aikata ayyukan zagon ƙasa ga jam’iyyar, yin kalaman cin fuska ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa, da wasu ayyuka da ake ganin za su haifar da rikici da rashin jituwa a cikin jam’iyyar.
Dakatarwar, kamar yadda takardar ta bayyana, tana bisa doka da tsarin jam’iyyar PDP ƙarƙashin sashe na 59(1)(a).
Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya kasance jigo a jam’iyyar PDP tun kafuwarta a shekarar 1999, inda ya rike mukamai daban-daban, ciki har da zababben Sanata da kuma zababben Sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Jam’iyyar PDP a Katsina ta tsinci kanta cikin rikici tun bayan shigowar Sanata Yakubu Lado Danmarke. A halin yanzu, jam’iyyar ta rabu gida biyu: ɓangaren Sanata Yakubu Lado da kuma ɓangaren Sanata Umar Ibrahim Tsauri.
Katsina Times
@www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar Labarai
@www.taskarlabarai.com