KANSIEC ta rage kudin fom na masu takara a zaben kananan hukumomi a Kano
- Katsina City News
- 13 Sep, 2024
- 408
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC ta rage kudin fom ga masu neman takarar shugabancin karamar hukuma da kujerar Kansila.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya sanar da cewa yanzu masu neman kujerar shugaban karamar hukuma za su biya Naira Miliyan 9 a yayin da masu neman kujerar Kansila za su biya Miliyan 4.
Ya kuma kara da cewa su ma abokan takarar ciyamomi za su biya Naira miliyan 9.
Daily Nigerian ta rawaito cewa tun da fari dai hukumar ta sanya Naira Miliyan 10 da Miliyan 5 ga masu neman kujerar Ciyaman da Kansila a zaben.
Rashin gamsuwa da kudaden ne yasa jam'iyyun adawa suka garzaya gaban kotu inda suka samo umarnin kotun da ya dakatar da karbar kudaden.
Da yake jawabi ga manema labarai a ofishin hukumar a yau Juma'a, Farfesa Malumfashi ya ce KANSIEC tayi biyayya ga umarnin kotun.