Kungiyar KADI A jihar Katsina Ta Tallafawa Masu Lalurar Tarin Fuka
- Katsina City News
- 13 Sep, 2024
- 202
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times. Satumba 6, 2024
Kungiyar "Katsina State Development Initiative" Ta Hannun Kamfanin Easy Engineering na Alhaji Yahaya Ibrahim ya Tallafawa Masu Lalurar Tarin Fuka da Magani da Takunkumin rufe Fuska.
An mika gudunmawar ne a karamar asibitin Gwamnati dake Kofar Kaura a birnin Katsina.
Da yake mika gudunmawar a madadin kungiyar KADI Malam Umar Sani Audi, ya bayyana irin Ayyukan da kungiyar ta sa a gaba na Tallafawa Masu Lalurar musamman Tarin Fuka, tare da kuma wayar da kai ga al'umma akan tallafawa da abinda Allah ya Hore masu.
Sana yace "Mun jagoranci mika wannan gudummawar Magani da Takunkumin rufe Fuska da Kamfanin Easy Engineering, na Alhaji Yahaya Ibrahim ya bayar ta hannun kungiyar, kuma yace ba wai ya tsaya haka ba, zasu ci-gaba da bada irin wannan gudummawar lokaci zuwa lokaci"
Da yake karbar Magungunan Shugaban bangaren Tarin Fuka na ma'aikatar lafiyar Jahar Katsina Dakta Mukhtar Aliyu ya bayyana cewa
"A kaidar wannan cuta ta TB, anayin gwaje-gwaje da Bada magani kyauta ne sannan Gwamnati na bakin kokarinta, Amma duk da haka, ana maraba da irin wannan gudummuwar domin a hada karfi da karfe wajen ganin anci nasarar yaki da wannan Cuta" Dakta Mukhtar yayi fatan Alheri tare da godiya akan wannan gudummawa. An mika wannan gudummawa a Bangaren Tarin Fuka na ma'aikatar Lafiya ta Jahar dake karamar Asibitin Kofar Kaura bisa rakiyar wakilan Easy Engineering, Alhaji Abdu da Alhaji Basiru, a ranar Juma'a 6 ga watan Satumba da ya gabata.