An bayyana Hon. Isma’il Usman Yandaki a matsayin Jagoran Ci Gaban Al’umma a Karamar Hukumar Kaita
- Katsina City News
- 11 Sep, 2024
- 346
An bayyana Hon. Isma’il Usman Yandaki, shugaban gidauniyar Garkuwan Kaita Charity Foundation, a matsayin wanda ya kawo cigaban al’umma ba tare da rike wata kujerar mulki ba a karamar hukumar Kaita.
Wakilan gidauniyar daga mazabu goma na karamar hukumar Kaita ne suka bayyana haka yayin kaddamar da fara ayyukan gidauniyar, wanda suka haɗa da samar da makarantu na firamare da sakandire, rijiyoyin burtsatse na sola da kuma injinan samar da wuta ga rijiyoyin, domin samar da ruwan sha ga al’umma.
Wakilan sun yaba wa Hon. Isma'il Yandaki bisa kokarinsa na kawo ci gaban al'umma ta hanyoyi daban-daban, wanda suka ce ba a taba samun irinsa ba a tarihin Kaita, duk da cewa ba ya rike da mukamin gwamnati. Sun nuna matukar sha'awarsu kan yadda ya sadaukar da dukiyarsa daga kasuwancinsa domin taimakawa al'umma, yana samar da ayyukan ci gaba kai tsaye.
A nasa jawabin, Hon. Isma'il Yandaki ya ce ya dauki alkawarin taimakawa al'ummar da yake cikinta, ko da yana rike da mukami ko ba mukami. Ya kara da cewa gidauniyar da ya kafa bata siyasa bace, kuma baya shirin tsayawa takara. Yana kuma goyon bayan dukkan shugabannin da aka zaba tare da yi masu fatan alheri.
"Ina fatan gidauniyar za ta taimaki marayu, matasa da masu karamin karfi. Muna tallafa wa sama da marayu dari da ke karatu kyauta a makarantar da muka samar, kuma a bangaren samar da ruwan sha, naira goma kacal ake biyan domin kula da cibiyar," inji shi.
Daga karshe, Hon. Yandaki ya jaddada cewa babban burinsa shi ne taimakawa al’ummar Kaita ta kowane bangare, ba tare da bambancin siyasa ba. Ya kuma tabbatar da goyon bayansa ga duk wani yunkuri da zai kawo ci gaba ga karamar hukumar.
A taron kaddamar da ayyukan gidauniyar, manyan baki kamar Sarkin Fawan Dankama, Alhaji Ali, Hon. Murtala Yanhoho, Hon. Ali Kure Kaita, da Hajiya Zainab Isa Sulaiman sun gabatar da jawaban yabo. Malam Bishir Sai’du Kaita, wakilin karamar hukumar Kaita, ya tabbatar da sahihancin ayyukan da gidauniyar ta samar domin amfanin al’umma.
A cikin wakilan gidauniyar da suka halarci taron har da mataimakin shugaban karamar hukumar Kaita, Hon. Mu'azu Abdu Dankama, tsofaffin 'yan majalisar jiha, tsofaffin kansiloli, da sauran 'yan siyasa da suka yi gwagwarmaya a bangarori daban-daban.