AN SAKO MUTANEN GARIN MAIDABINO: BAYAN BIYAN KUDIN FANSA NAIRA MILYAN 36...
- Katsina City News
- 11 Sep, 2024
- 456
...Saura mutane biyar suka rage a wajen "yan ta addar.
Daga Muazu Hassan
Katsina Times ta samu tabbacin barayin daji da suka afka garin Maidabino dake karamar hukumar Danmusa a jahar Katsina,Suka tafi da magidanta mutane 85,mata da maza,banda na goye an sako mutane tamanin a cikin su.
Binciken da Katsina Times tayi a garin na
Maidabino ya gano barayin sun sakama kowane magidanci kudin fansar naira dubu dari uku, daga baya suka kara farashi zuwa kowane magidanci, akan naira dubu dari hudu da Hamsin.
Katsina Times sun gano barayin basu amshi kudin fansa akan jarirai da kuma wadanda ke goye ba.kuma da aka fara kai kudin, mata masu goyo da ciki suka fara saki.
Katsina Times ta gano cewa kowane magidanci shine yayi kokarin sako nashi da aka kama, wasu Katsina yanka bangarorin gonakin su, suka sayar, wasu kayan gona,wasu kuma suka shigo cikin gari suka nemi taimakon "yan uwa da abokan arziki.
Katsina Times ta gano, Mutane biyar suka rage wajen wadannan miyagun barayin na daji.mutanen biyar an kasa hada kudaden da za a amso su.
Katsina Times tayi magana da magidanta biyar da aka sako, amma sunki magana saboda tsoron abin da zai biyo baya.cewa sukayi.." kun San har yanzu muna garin Maidabino kuma bamu fi karfin barayin nan, su sake dawo wa ba, don haka don Allah ku kyale mu"
Jaridun Katsina Times sune suka taba buga wani bidiyon wadannan bayin Allah a lokacin suna a daji tare da wadannan miyagun barayin.
Sama da mutane milyan daya suka ga bidiyon tsakanin shafukan yanar gizo da na sada zumunta na jaridun Katsina Times da kuma wadanda suka yi ta daukar shi suna watsawa.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
All in All social media platforms