Gwamnan Zamfara ya Kaddamar da sake gina Babban Asibitin Talatar Mafara
- Katsina City News
- 08 Sep, 2024
- 201
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta kiwon lafiya a jihar, tare da bayyana irin rawar da manyan asibitoci ke takawa a fannin kiwon lafiya.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne gwamnan ya ƙaddamar da aikin sake gina babban asibitin da ke cikin Ƙaramar Hukumar Talata Mafara tare da gina katafaren ginin da zai ɗauki gadaje 200.
Mallam Yahaya Abdulkarim, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato ne babban baƙo na musamman a wajen bikin ƙaddamarwar.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka yi watsi da babban asibitin Talatan Mafara, inda ya nuna cewa asibitin na fama da rashin isassun kayan aikin jinya da kuma rashin kyawun ababen more rayuwa a tsawon shekaru.
Gwamna Lawal ya bayyana cewa, gwamnatocin baya sun yi watsi da harkar kiwon lafiya gaba ɗaya, wanda hakan ya sa gwamnatinsa ta fara aiwatar da aikin gyara fannin.
Ya ce, “Da yardar Allah yau na zo ne domin cika alƙawarin da na ɗauka a watannin baya lokacin da na ziyarci wannan asibiti da jami’ar jihar. Bisa la'akari da halin da ake ciki a wannan cibiyar kiwon lafiya, na yi alƙawarin gudanar da aikin sake gina shi gaba ɗaya don samar da babban asibitin da ya dace da babban gari kamar Talata Mafara.
“Gwamnatinmu ta ba da fifiko wajen farfaɗo da rugujewar ababen more rayuwa a matsayin muhimmin ginshiƙin ajandar kawo sauyi. Mun sanya ilimi da kiwon lafiya a kan gaba, tare da sanin matsayinsu wajen cigaban al'umma. Wannan asibiti ɗaya ne daga cikin wurare da yawa da ake ginawa don samar da yanayi mai kyau wajen samar da nagartaccen ayyukan kiwon lafiya.
“Gwamnatinmu ta tsaya tsayin daka wajen sanya hannun jari a fannin kiwon lafiya, tare da fahimtar muhimmiyar rawar da manyan asibitocin ke takawa a tsarin samar da lafiya. Suna aiki a matsayin muhimman hanyoyin da suka haɗa cibiyoyin Kula da Lafiya na Farko da Manyan Cibiyoyin Kiwon Lafiya.
“Aikin da muke ƙaddamarwa a yau ya ƙunshi gina asibiti mai ɗaukar gadaje 200 tare da samar da kayan aiki na zamani domin inganta lafiyar al'umma.
“Ya haɗa da gine-gine kamar haka: Wuraren zaman jira, sashin bayanai da asusun ajiya, sashen kula da yara, ɗakin jinya na maza, ɗakin jinya na mazan da aka yi wa tiyata, ɗakin gwaje-gwaje, ɗakin tiyata, ɗakin gwaje-gwajen haƙori, ɗakin karɓar magani, ɗakin jinya na matan da aka yi wa tiyata, ɗakin jinya na mata, sashen ENT. Ɗakunan haihuwa guda biyu tare da ofishin babbar mai karɓar haihuwa, ɗakin wankin ciwo, ɗakin zaman ma'aikatan jinya, ofishin Babban Manajan Daraktan Kiwon Lafiya na asibitin tare da ofishin sakatarensa, ofishin likitan haƙori, ɗakin canja kaya na mata, ɗakunan ganin likita guda biyar, ɗakin ICU, rukunin na'urar X-ray, sashen kai marasa lafiya na gaggawa 'Accident & Emergency (A&E)', sashen kula da masu juna biyu, wurin cin abinci, da ofishin matron.
“Za a kammala shi cikin watanni shida, inda kamfanin Abdulwahab Razaq Memorial Ltd ya kasance a matsayin ɗan kwangilar. A halin da ake ciki, abin farin ciki ne na musamman na gayyato babban baƙon mu, mai girma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim, Magajin Rafin Sokoto, domin ƙaddamar da aikin gina wannan asibiti a hukumance.”
Tun da farko, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim, ya yaba wa gwamna Dauda Lawal bisa bai wa ɓangaren kiwon lafiya fifiko a cikin ayyukan da gwamnatinsa ta sa gaba. "Na yi mamakin lokacin da gwamnan ya shaida min cewa an riga an sayo dukkan kayan aikin da za a yi amfani da su a Babban Asibitin, wannan abin yabawa ne matuƙa."